ZINARIYAR MACE: Hanyoyin Da Zaki Bi Ta Yadda Zaki Gyara Gashin Ki Yayi Tsawo !!!


 

Ma'asumah Nigeria news update 

Hadin danyen kwai:


Abin bukata:-


      Kwai Danye. 


      Roba mai Kyau mai dan fadi 


Kisamu wannan kwan naki saiki dauko wannan roba taki saiki fasa wannan kwan ki cire kwaiduwar kwan ma' ana wannan yallon abin na ciki ki ajiye gefe daya, saiki juye farin ruwan kwan a wannan roba taki. Idan gashin naki da dan yawa saiki fasa kwan kamar uku-kodai yanda yasamu. Saiki dinga diban wannan farin ruwan kwan kina shafeshi a gashin naki, har saikin tabbatar cewa ruwan kwan ya ratsa ko ina cikin gashin naki. Saiki barshi tsawon mintuna ashirin ko talatin sannan ki wanke kan naki da sabulu mai kyau kina iya amfani da sabulun Allo berra. Kada kimanta cewa gashi yakan sanya mazaje kara kaunar matayensu . 


Hadin man amla:Abubuwan da za a bukata


     Man Amla

     Zuma

     Ruwan dumi


 


A zuba cokalin amla biyu a roba.


Sannan sai a zuba rabin cokalin zuma a cikin amla.

A sanya cokalin ruwan dumi kamarbiyu zuwa uku A juya hadin har sai sun cakudu da juna.A taje gashi kamin a shafa wannan hadin a fatar kai A jira na tsawon mintuna talatin.A wanke kai da man wanke gashi (shampoo).hmmmm saikin bani labari.


Ummu Radiyya.....✍🏻✍🏻

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post