Kogin So, Fadawa Ba Wahala, Fitowa Lafiya Sai Mai Sa'a. Kashi Na Biyar (5)






Rbtw:J. I. R.

Haka soyayyarsu ta ci gaba da tafiya lami-lafiya,ba tare da wani abu ba.Ahmad ya muhimmantar da soyayyarsu fiye da yanda ake tsammani,har ya kai da Ahmad ya zama wannan abun da ake kira "Dan kwali,ya ja hula",domin har school shi yake rakata wata rana,wata rana kuma ya je ya daukota.Suna tafiya suna shan soyayyah,abun ban sha'awa.Akwai wata rana da Ahmad ya kira Zainab tana school,akan yana son ganinta,yana mai cewa:"Masoyiyata na zam mai nasara,a sannu-sannu kin bani ruwan zuman kauna.Haqiqa soyayya ta zamo min abun alfahri.Kina ina hasken idanuwata?,ina son ganinki".Zainab ta ce:"Masoyina,kuma farin-ciki na,ina school.Ni zan baka labari, don kuwa soyayyarka ita ce rabo mafi girma da na samu a rayuwa,ina alfahri dakai jigon rayuwa".Ahmad ya ce:"Lallai kam,ra'ayinmu ya zam daya,ina tabbatar miki ba zan baki kunyaba,kece zabi na daya tal.Allah ya barmu tare Saurauniyata,yanzu dai kar na ja ki da surutu in kun gama lecture na zo na dauke ki a mashin dina,na kaiki gida don ban son ki wahala min".Zainab ta ce:"Uhmm.Qalbi na,kamar ka sani dazu mu fito daga last lecture,yanzu kazo Main gate".Ahmad ya tafi ya je ya dauko muradinsa,ya kai ta har gida.Su yi sallama ya koma gida.

Bayan ya koma gida,ya huta.Se ya nema ummansa don ya bata labari,cewa ya samu macen da yake so da aure.Ya baiwa ummansa labari yana cewa:"Umma haqiqa zan miki albishir,da cewa na sama miki sarkuwa tagari,sunanta Zainab".Ummansa budan bakinta ta ce:"Lahh!,ashe Ahmad zan ji wannan labarin mai dadin ji,Allah ya nuna mana,ya kaimu lokaci mu sha biki". Ahmad cikin farin ciki ya ce:"Amin ummah nah".

Mu hadu a kashi na 6,in Allah ya hadamu.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post