Tambayoyi Shida (6) Ga Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari !!!


 

Daga: Nura Ibrahim Khalil, Zaria

inshaallahulkareem@gmail.com

30/10/2020


Ranar larabar da ta gabata wato 28 ga watan October 2020, BBC Hausa, ta wallafa a shafinta na facebook cewa: kuna iya aiko da tambayoyin ku da suka shafi zanga-zangar #EndSars da abubuwan da suka biyo baya, ga shugaban Nigeria Muhammad Buhari.


Na aika tambaya game akan wannan maudu'i, har ya zama abin muhara, amma sai na ga ya dace in fito wajen wannan shafin don in kara warware wadannan tambayoyi domin gaskiya halin da Nigeria ta shiga a wadannan shekaru shidda a matsayi na na musulmi kuma da Nigeria yana damuna sosai.

-----------

(1) Sanin duniya ne cewa an sojojin Nigeria sun iso Zaria da sanyin safiyar asabar 12 ga watan December 2015 kuma suka fara yi wa almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky kisan dauki dai-dai a harabar cibiyar harkar musulunci da ke lamba 1, Sokoto road da ke G.R.A Zaria kuma gaba baya suka fadada wannan hari zuwa kisan kiyashi, wanda ya yi sanadiyar kisan mutane fiye da dubu, da rushe duk wani gini ko kona duk wata dukiya mallakar wannan harka. an fita da Shaikh Zakzaky da mai dakinsa cikin jinin harbin da aka yi musu bisa tsammanin ma basu raye, daga bisani kuma aka koda gidan nasa da ke anguwar Gyallesu Zaria. daga baya harkar ta shigar da kara kuma kotu ta ce a sake su a biyasu diyya amma Gwamnatin Nigeria ta ki bin umurnin kotu kuma ta yi gum da bakinta.


Tambayata a nan shine: Wannan Gwamnati karkashin Muhammadu Buhari tana ikirarin bin doka da Oda. Shaikh Zakzaky da almajiransa sun yi wani laifi ne aka sa sojoji suka yi masu haka? idan kuma laifi suka yi mai ya sa ba kai su kotu alkali ya hukunta su dai-dai da laifukansu ba? ko kuwa maganan cewa wannan Gwamnati na bin doka da oda kawai a baki ne?


(2). Duk duniya kowa ya san irin rashin tsaron da ke Nigeria kuma har yanzu ana bi kauyaku da birane ana yi wa 'yan Nigeria kisan kare dangi, ga kwashe dukiya da kona kadarori da sunan 'yan bindiga, gar maganan a kama mutum a ce sai an biya kudin fansa wanda abin har kai ga yana shafan 'yan sanda da sojojin kasar, sannan ga zancen boko haram ya ki ci ya ki cinyewa, sannan na karanta a wata jarida cewa za ka gyara Nigeria a cikin shekaru biyu kacal, amma gashi wankin hula ya kai ku dare. meyasa ka ki amsa kiran 'yan Nigeria da kuma na wasu daga kasashen waje na cewa ka canza manyan hafsoshin tsaron soji na Nigeria tunda ya bayyana a fili cewa sun gaza, kamar yadda takwaranka Muhammadu Isoufou na jamhuriyar Niger ya yi, likacin da aka kai wa sojin sa hari aka kashe kusan saja dari biyu ba?


(3). Duniya ta ga irin alkawuran da ka yi wa 'yan Nigeria lokacin yakin neman zabeka a 2015, inda kake cewa idan talakan Nigeria ya sayi litar man fetun naira hamsin #50 an kware shi, ka daga taliya a kano, sannan ka sha fada a yakin neman a zabenka cewa: "mai su aski, da walda da kuma masu sayar da ruwan sanyi basu samun riba saboda sai sun sayi generator, kuma sai sun sanya mai kafin ya yi aiki, saboda da haka basu samun ribar da ta kamata," kuma ka yi alkawari samar da wutar latarki isashshe, amma har yarzu gwara ma jiya da yau kuma babu wani cikakken bayani, muna bukatar cikakken bayani akan wajenda aka kwana, ko gwamnatinka ita ma ta gaza ne kamar yadda kuka zargi gwanatocin baya?


(4) Ka sa an rufe iyakokin Nigeria da kasashe makwabta, wanda wannan ya sabbaba mummunan tsananin. rayuwan talakawa a Nigeria, kayan masarufi suka yi tashin gwauron zabi, sakamakon haka mutane dayawa sun samu karayar arziki, wasu sun mutu, wasu sun bar Nigeria har da kananan yara. duk da cewa muhamman mutane a ciki da wajen Nigeria suna ta kira cewa a bude tunda rufe iyakokin bai magance matsakar tsaron da Nigeria din ke ciki ba, amma shiru ka ke ji. ko za a fada mana hikimar sanya mutane a irin wannan hali musamman ga irin shugaban da talakawa suka so shi kamar kai?



(5) An yi zangazangar #EndaSars na kusan tsawon mako biuy a Nigeria, masu zangazar suna na sharudda biyar ciki akwai yi wa rundunar SARS din garambawul bisa zargin cin mutuncin mutane fiye da kima da kuma sauransu, kamar rashin aiki ga matasa, rashin tsaro a Nigera da dai sauransu. Ka saurare su kuma ka ce akan doka suka yi komai (alhali kina cewa 'yan Shi'a basu da daman gudanar da tarukansu zanga-zangar lumana da suka saba yi cikin tsaro) sannan ka yi alkawarin baya masu bukatunsu, sannnan har ta'aziyya ka yi masu kan wadanda aka kashe a Lekki Toll Gate kuma duniya ta shaidi lallai ka damu. meyasa baka bayyana damuwarka ga irin abubuwan cin kashin da ake yi wa yankin arewacin Nigeria, duk da cewa daga can ka fito, amma a bayane ka fi fifita yankin kudancin Nigeria?


(6) An yi kullen COVID 19 na watanni kuma an bada tallafin abinci a raba wa 'yan Nigeria kodayin ministan aiyukan jin kai ta ce an ba jihohi a kan lokaci, to amma meyasa sa a matsayinka na shugaban kasa idan kuka bada aiki na takakawan da suka zabe ku Baku bibiya ku gani an yi ko ba a yi ba, sai dai talakawa su yi ta koka a gidagen radio da jaridu akan alkawuran da kuka dauka masu lokacin yakin neman zabe da kuma muhimman aiyukan da suka hau kan ku, amma ba za ku dauki mataki ba?


Da fatan za mu ji amsoshin wadannan tambayoyi a kan lokaci, kafin mu kara bijiro da wasu nan gaba, don tambayoyin suna da yawa, tunda ana mulki ne na demukradiyya mai bada 'yancin fadin albarkacin baki, ba mulikin soja ake yi ba...

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post