Duk Wanda Ke Tuna Mutuwar Sa, Zai Gujewa Duniya


 

@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @


Babu wani abinda ke sa mutum yaso duniya da kuma fifitata kan komai fiye da rashin tuna mutuwarsa. Duk wanda ke tuna cewa zai mutu ya bar duniya kuma ya tarar da abinda ya aikata ba zai dauki duniya gidan zama ba. 



Ita mutuwa ba burinta koda kuwa mutum ya aikata kyawawan aiki, domin in mai kyawawan ayyuka ne tsohon rayuwarsa na qara masa kyautata lahirarsa ce. 


Ya zo cikin Tafsirul-Qummy dangane da ayar nan dake cewa, 


👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼👇🏼


 1- فس، تفسير القمي‏



 " فَتَمَنَّوُا الْمَوْتَ إِنْ كُنْتُمْ صادِقِينَ‏ ."


" KUYI BURIN MUTUWA IN KUN KASANCE MASU GASKIYA (cikin abinda kuke fadi ko kuke aikatawa) ."



Sai yace, 


قَالَ إِنَّ فِي التَّوْرَاةِ مَكْتُوبٌ‏

أَوْلِيَاءُ اللَّهِ يَتَمَنَّوْنَ الْمَوْتَ ثُمَّ قَالَ‏



" Lalle an rubuta cikin Attaura cewa Waliyyan Allah na burin mutuwa. " Sa'annan yace, 



 إِنَّ الْمَوْتَ الَّذِي تَفِرُّونَ مِنْهُ فَإِنَّهُ مُلاقِيكُمْ‏


" LALLE ITA MUTUWAR NAN DA KUKE GUJE MATA MAI HADUWA CE DA KU (gaba-da-gaba) ."


Ma'ana Idan ma kuna guje mata ne za ku hadu da ita a gabanku, kenan gujewar taku daga gare ta qara kusantaka kuke mata. 



Sannan kuma ya zo cikin riwaya daga tuqe kan Abiy Ubaidata yace, 


- ين، كتاب حسين بن سعيد و النوادر ابْنُ مَحْبُوبٍ عَنْ أَبِي أَيُّوبَ عَنْ أَبِي عُبَيْدَةَ قَالَ: قُلْتُ لِأَبِي جَعْفَرٍ ع جُعِلْتُ فِدَاكَ حَدِّثْنِي بِمَا أَنْتَفِعُ بِهِ فَقَالَ يَا أَبَا عُبَيْدَةَ مَا أَكْثَرَ ذِكْرَ الْمَوْتِ إِنْسَانٌ إِلَّا زَهِدَ فِي الدُّنْيَا.



Na cewa Abu Ja'afar (A. S), na sanya fansa gare ka, ka bani labari game da abinda zai amfanar dani , yace, 


" YAA BABAN UBAIDATA ! MUTUM BA ZAI YAWAITA TUNA MUTUWA BA FACE YAYI GUDUN DUNIYA ."


بحار الأنوار (ط - بيروت)، ج‏6، ص: 126



Duk wanda kaga adon duniya ce ta qawata shi da kuma neman mulki da danniya, to, lalle ba ya tuna mutuwarsa. Wanda ke tuna mutuwa za ka ganshi yana gujewa duniya. 


Daga wakilanmu na Bauchi zone. 


Tare da Ado Isah Guda. 

          08137925034


30th October, 2020/ 13th Rabi'ul-Awwal, 1442.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post