Kwadayi Yasa Malamai Qasqanci Da Rasa 'Yanci!!!


@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

GA ALLAH DA MANZONSA DA KUMA MUMINAI KADAI IZZAH TAKE

ko da a dokar qasa an bawa kowa damar fadar ra'ayinsa ko fahintarsa akan komai, ko da kuwa akan kowanene.

Dokar muslimci takan sassaba a wasu gurare cikin wani tsari da yazo daga wanin Allah, domin muslimci ya koyar damu ladabi da biyayya cikin Al'amarin jagoranci.

Ba zai taba yiwuwa ga mumini ya fadi wata magana ta muni ga jagoran muslimci ba, ko da kuwa fahintarsa ta sha bamban da tasa fahintar. Wannan dalili yasa aka zargi Sahabin nan da ya yiwa Annabi (S. A. W. W) zargin rashin yin adalci cikin rabo.

A dokar dimokuradiya ta wannan zamani kuwa za a iya fadar komai akan wani gwargwadon yadda aka fahince shi. Bisa wannan dalili yasa kake gani wasu na fitowa suna cewa babu adali kamar Buhari, wasu kuma ke cewa ba a taba samun azzalumi marar imani da tausayi kamar Buhari ba tun bayan shudewar Fir'auna.

Idan muka koma kan taken (TITLE) din rubutunmu kuma muka kalli yadda malaman gwamnatin Banu Umaryyah dana daular Abasiyawa za muga cewa kwadayin duniya da abin hannun azzalumai ya hana malaman zamaninsu fadar gaskiya, kuma su kayi gaba da mai fadin gaskiyar don biyan buqatun kansu.

Su kuma malaman kirki su kayi jayayya da zalunci da azzalumai wanda hakan yayi sanadin karkashe wasun su, wasun su kuma aka cutar dasu iya cutarwa.

Wannan abu shine yazo wannan zamani, kwadayayyun malamai ne ke shanawarsu a fadar azzalumai wanda hakan ya janyo musu qasqanci. Su kuma magada Annabawa ake cutar dasu, sai dai kuma su ke da izza a idon duniya, da kuma daukaka wajen Allah.

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

          09039791509

Sunday 6th Sep, 2020/ 18-1-1442.
DOMIN CIGABA DA SAMUN LABARANMU KU BIYO A SHAFUKAN SADA ZUMUNTA NA 

@FACEBOOK: https://web.facebook.com/Maasuma.com.ng/

@TWITTER: https://twitter.com/MaasumahNews/

DOMIN BAMU SHAWARA KO AIKO MANA DA LABARI KUYI MAGANA TA ADRESHIN

@EMAIL: maasumalabari@gmail.com

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post