Tunda Na Samu Mlm Zakzaky (h)Sai Allah (T) Ya Raba Ni Shiga Rudu Irin Na Nigeria da 'Yar'Yarnta ...!!


...Umar Hassan Gololo...

Na saurari jawabansa,na karanta jawabansa,na kalli jawabansa dabam-dabam,jawabi ne na ganawa da Mutanen gari, Malaman Addini, Malaman Boko da 'Yan-boko, dalibai,'Yan-jaridu, Maza da Mata,Yara da manya na kuma fahimci lallai Malam Zakzaky(H) Yana nemawa Mutane mafita ne a Duniyarsu da Kuma kyakkyawan sakamako a lahirarsu.

Ban taba jin Malam Zakzaky(H) ya Fadi magana Yau gobe ya dawo yace ba haka ba.
Ban taba ji Malam Zakzaky(H) Yana kafirta Musulmai ba, bilhasali ma har kiristoci mafita yake nema musu a Wannan addinin.
Na lura dukkan wanda yace abi Allahu Ta'ala a dukkan rayuwa to wahala yake sha Koda shi Annabi ne ballantana Wanda ba Annabi ba..

Na lura dukkan Gwamnatin zalunci tana fada ne da Wanda yake fadawa Jama'a gaskiya.

Na lura dukkan Malamin da zai je neman alfarma gidan Gwamnati to ba zai taba fada mata gaskiya ba ballantana kuma yace ga halin da talakawanta suke ciki..

Malam Zakzaky(H) tun shekaru arba'in da suka wuce yake cewa babu wata hanyar da Mutane zasu fita daga kangin bautar azzalumai idan ba Musulunci ba,har yanzu kuma a haka yake bai sauya ba,akan Wannan Kiran aka daure shi,aka azabtar dashi,a Wannan Kiran aka kashe daruruwan Almajiransa da 'ya'yansa yanzu haka Yana tsare saboda Kiran da yake a komawa tsarin Allahu Ta'ala.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post