Sheikh Ibraheem Zakzaky (H) ya yi wa 'ya'yansa uku da suka rage a duniya, wato Sayyid Muhammad, Sayyida Nusaiba da Sayyada Suhaila, a ranar da sojoji suka kai hari gidansa, suka kashe kusan mutum dubu daga almajiransa, kuma suka kashe 'ya'yansa maza uku, da babbar Yayarsa, suka harbi matarsa, shi ma suka yi masa ruwan harsashi, da yake bai dauka zai rayu ba, ya yi kebantacciyar Wasiyya ga 'yarsa Sayyid Suhaila wacce yake tare da ita a lokacin.
Ta ce, daga cikin Wasiyyarsa gareni ya ce; "In kula da Sallah, sannan mu dau fansar abin aka yi mana, kar mu kyale abin da aka yi mana ya tafi (a banza), kar mu yi shiru akan abin da aka yi mana. Sannan in yi hakuri, in kalli rayuwar Sayyida Zainab (SA), in yi hakuri irin nata, in yi rayuwa irin yadda ta rayu. Ya yi batun komawa makaranta, yana wannan halin ya rika karfafamu ni da Sajida akan muhimmancin ci gaba da karatunmu, ya ce in mun rayu mu tabbata mun koma makaranta, kar mu ce ba za mu koma ba, kar mu tsayar da komai namu dan abin da ya faru, amma kar mu kyale abin ya tafi a haka nan (Siddan)."
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Jagoran Gaskiya
