BUHARI YAYIWA MUSULUNCI BABBAR ILLA

 BUHARI YAYIWA MUSULUNCI BABBAR ILLA.

sanin kowa ne cewa zaben 2015 anyi sa ne tsakanin Arewa da Kudu, Musulunci da Kafurci, ta yadda da yawa daga cikin Malamai su ka rinka kiran mutane da su fito suyi jihadi badon komai ba sai saboda yadda Gwamnatin Goodluck ta mayar da Al'ummar Arewa saniyar ware da yadda yake ko in kula da kazamin ta'addancin BokoHaram a wancan lokaci.

Bansan ko sau nawa mukayi Alqunuti ba a SBRS Funtua lokacin muna karatu a can a karshe karshen 2014 badon komai ba sai don san Bawan Allah nan Buhari da kuma nuna Adawa da Gwamnatin can ta baya, mutane da yawa sun tuttura kudin su hasali ma Buhari siyasan masa fom akayi don kawai mutane suna ganin sa a matsayin mutum mai adalci ana ganin idan ya hau zamu samu saukin rayuwa.

A "campaign" din sa yace mana idan ya hau kan karagar Mulki zamusha roman demokradiyya, litar man fetur zai dawo 50, Taliya ma haka, zaa biya yan Najeriya 5k duk wata, BH zata zama tarihi a shekarar sa ta farko dadai wasu tatsuniyoyin wanda har yanzu ya kasa cika ko daya.

Al'ummar kudu sai suka koma gefe suna kallon mu suna dariya domin yama fi wa Yankin nasu aiki fiye damu, bincike ya nuna Yankin Yarbawa kawai sun sami kaso 1 bisa 3 na ayyukan mulkin sa gaba daya wanda Arewacin Nigeria ta fisu taka muhimmiyar rawa wajan kawo Gwamnati mai ci amma duk da haka ya watsawa Arewaci kasa a ido.

Abun takaici sai Malamai wanda sukayi mana ingiza mai kantu suka sakamu muka zabi Buhari a matsayin Shugaba, duk da halin da ake ciki sunki fitowa su fada masa gaskiya kullum sai kokarin kareshi saboda suna zuwa Villa su amshi na goro, muddin baza a badawa Shugaba gaskiya ba to babu fatan wani sauyi daga wannan Shugaban shiyasa gashi kullum jiya a yau.

A yanzu Yankin Arewa shine koma baya wajan Arziki, Ilimi da zamantakewa ga babban Matsalar tsaro da kullum muke ciki dukda Shugaban Kasa dana sojoji da yan sanda, custom da Emigration duk sun fito daga wannan Yankin ne, wannan abun kunya ne matuka. Allah ya kawo mana dauki

___Muhd Aliyu Indianprince

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post