Abubuwan Dake Jawo Taɓarɓarewar Aure A Ƙasar Hausa Na Biyu (2)


ABU NA BIYU

ZAFIN KISHI

Kishi halittane da Allah (S W T) Ya halicci ko wanne mutum tashi musama ma ɗa namiji wanda shi kishinshi kariya yake ba mace duk da cewa mata sun are sun yafe kuma ba wanda ya isa yace mace kada tayi kishi, sai dai kada kishin yayi tadirin da zai sa mace tasaɓawa Allah (S W T) ta hanyar zuwa wajen bokaye ko malalaman tsubbu, don a cutar da abokiyar zamanta ko ta hana mijinta ƙara yin aure alhalin yana son yaƙara, ko ta rinƙa nuna mashi wasu munanan halaye har yagama gara yarabu da ita ya huta.
Kuma, yawancin abin da kesa mace zafin kishi shine, tsoran cutarwa da kishiya zatayi mata intazo, ko don hassadar kada suyi tarayya da ita acikin abinda mijinta yake dashi na dukiya, ko abinda zata samu nagado idan mijin yarasu. Kuma irin wannan tsora ne kesa wasu matan suyi ta ramewa, ko suje wajen boka ko malamin duba, wanda wannan halakane agaresu Allah yakaremu.

Sai dai, matar Bahaushe aƙasar hausa da kayi mata ƙarin abukiyar zama, gara wai duk abinda mijinta zaiyi abayan idanta yana iyayi batadamuba,har wasu nacewa da kishiyar gida gara ta waje
Don kuwa harcewa suke yi ƙazantar da ido baiganiba tsaftace. Amma acikin hikimar da Allah ( S W T) Yace maza su auri mata har huɗu, shine da araya sunnar Manzan Allah ( S A W W) kuma arage adadain matan da basuda aure tunda Manzan Allah ( S A W W) yanuna ahadithi cewa yana daga cikin alamomin tashin alƙiyama mata zasufi maza yawa. Sannan matar zata iya mutuwa ta bar ƴa ƴa, ko kuma ta kamu da rashin lafiya, ko tafiya zuwa unguwa da takamata. Amma matar da zatace mijinta yayi ta morewa da matan banza awaje in dai ba zaiyi mata abokiyar zamaba zamaba, to wannan mata batada hankali, domin yarda asaɓawa Allah (S W T) sannan kuma za a iya aje aɗebo cuta akawo mata hargida. Saboda haka, zafin kishi nasa miji yaji mace ta isheshi har ma yaga gara yarabu da ita ya huta.

NASIHA GA MATA yakamata kukasance masu tawakkali ako da yaushe, sannan ta rinƙa yin addu a Allah yarage mata zafin kishi alokacin da tayi azumin nafila ko duk wani lokaci da yatabbata ana amsar addu' a. Kuma kada mace tashagaltu da abin da kishiyarta keyi na neman rigima da tashi hankali da ita maimakon haka, ta duƙufa da karatun Alƙur ani da abubuwan da zasu amfaneta aduniyat da lahirarta. Idan tana haka, to mijinta zai ƙara sonta kuma zata fi ƙarfin kishiyarta dake neman ako da yaushe su kasance acikin faɗa da bala' i. ZANCIGABA INSHA ALLAHU

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post