Tofa! Wata Sabuwa inji 'Yancaca. Majalissar Dinkin Duniya Zata Kirkiri Wata Kasa A Tsakanin Najeriya da Kamaru

Daga Muhammad Aliyu Indianprince

Majalisar dinkin duniya ta shirya tsaf domin kirkiran wata Kasa a tsakanin Najeriya da Kamarun daga ranan Laraba, 10 ga watan Junin 2020.

Za a sakawa kasar suna UNO (United Nations Organization) wanda zaiyi sanadiyyar rasa kauyaku 24 daga Najeriya.

Tsahon Shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo da shugaban kasar Kamarun Paul Biya  su suka sanyawa takardan yarjejeniyar kirkirar wata kasar a shekarar 2003 yayin da sakataran Majalisar a wancan lokacin Kofi Annan ya gayyace su.

National Daily ta ruwaito cewa sabuwar Kasar zata kai kallan fadin (28,214 square km) da akalla yawan mutane milliyan 20.

Sanarwan ta fito ne a ranan 26 ga watan Mayun 2020 a wata wasika da farfesa Martins Chia Ateh ya fitar wanda shine ke kula da lamarin Kafa Qasar a tsakanin Najeriya da Kamaru.

Ateh ya kara da cewa kasar zata hada da Yankin Bama, Gwoza, Ngala, kala/Balge, Dikwa, Madagali, Michika, Mubi North, Mubi South, Mayo/Belwa, Toungo, Ganye, Serti, Hong, Jada, Maiha da Kauyen Jada.

Yaya kuke ganin kirkiran wannan kasar a Yankin dake fama da rikicin BokoHaram, ko hakan zai kawo mana karshen Ta'addancin da muke fama dashi.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post