Haramta Almajiranci : Gwamnoni Sun ci Moriyar Ganga.

Haramta Almajiranci:  Gwamnonin Arewa sun ci moriyar ganga

Musulmi kake ko Kirista, babba kake ko yaro, ka sani ko baka sani ba, ka yarda ko baka yarda ba, matuƙar kai ɗan arewa ne almajiranci shine ƙashin bayanka har ma da arewacin Nijeriyar baki ɗaya! Nasan kasan cewa; har abada tarihi bazai manta da Sheikh Usman Bin Fodiyo ba gami da gudumawar da ya bayar wajen ci gaban arewa.

Zuwan Turawan mulkin Mallaka (colonial masters) Arewa, sun samu ƴan arewa da 'complete' tsari na addini, tarbiya, al'ada, kasuwanci, da jagoranci na mulki tun daga matakin kansila har zuwa shugaban ƙasa (sarkin musulmi), wanda almajirine ke jan ragamar  kuma ƙarƙashin tsarin almajiranci wanda a lokacin ƴan Kudu basu ma san me ake kira da riga ba ballantana wando!.

ALMAJIRANCI ALFAHARINMU ƳAN AREWA
Duk wani alfahari da kake yi tare da jin cewa; kai ɗan arewa ne, malami kake ko mai sarautan gargajiya, ko mai mulki kake to, almajiranci ne ya samar maka da duk wani tsari gami da ƴancin more rayuwar da kake ɗanɗanawa a yanzu ƙarƙashin da'awar Sheikh Usman Bin Fodiya. Kenan bai kamata a bar tsarin almajiranci ya lalace ba.

Zuwan turawa Nijeriya ne suka lalata tsarin almajiranci. Alokacin suka nuna Qur'ani ba yi da daraja. Suka nuna 'constitution' ne mafita. Suka nuna duk wanda ke karatun allo bashi da ƙima a idon al'umma, suka nuna mai karatun allo  a matsayin bagidaje to, tun daga wannan lokaci almajiranci ya fara shiga halin ni ƴa su.

ALMAJIRI BA  ƊAN TA'ADDA BA NE
Bincike ya nuna cewa, duk wani ta'addancin da ake yi a duniya babu wani wanda tsarin almajiranci ne ya samar da shi kuma ya zamo ɗan ta'adda, bilhasali ma idan kaga wani ta'addanci zaka taras cewa, wani ra'ayine na wani manhaja da ake kiransa 'nizamiyya' wanda wani ƙudiri ne da ya samo asali daga Ƙasashen waje amma dai ba tsarin karatun allo ba.

 Almajirai suna kan gaba wajen ciyar da kasan Nijeriya gaba ta fuskacin tattalin arziki da kuma abunda ya shafi ilmantarwa da kuma wasu ayyukan raya ƙasa da kuma zamantakewan al'umma (social well-being)
ALMAJIRI ƊAN ƘASA NE KAMAR KOWA
Almajiri shi ma ɗan Kasa ne, yana da cikakken ƴanci na samun ingantacciƴar ilimi, tarbiyya, kayan more rayuwa ds kamar sauran ƴan ƙasa.

Tunda hakane me zai hana a zamanantar da ilimin almajiranci ta yadda almajirai za su samu ilimi ba tare da sun wulakantaka ba. Suma a ciyar da su kamar yadda ake ciyar da sauran ɗalibai. A biya malamansu 'salary' kamar yadda ake biyan sauran malamai.

Almajiri Model Schools
A baya,  gwamnati ta yi yinkurin haɓɓaka karatun allo ta hanyar gina makarantun alluna a wassu daga cikin Jihohin arewacin Nijeriya me suna; Almajiri Model School, kuma ta ɗauki nauyin biyan malamansu albashi domin ci gaba da koyar da almajiran. Ina da tabɓacin cewa, idan gwamnati ta tallafa ma waɗannan almajiran yadda ya dace, tabbas suna da rawar da zasu iya takawa wajen kawo cigaba a cikin al'umma da ma ƙasa baki ɗaya kamar yadda Marigayi Sheikh Usman Bin Fodiyo da almajiransa suka yi.

-MKabeer Yahaya Daheer
08064672794
05/06/2020

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post