Yau 3 ga watan June shekara ta 2020, yayi dai-dai da ranar da Jagoran Juyin-juya halin Muslunci a Iran Ayatollah Imam Khumaini (Qs) ya bar Duniya. Imam Khumain yayi wafati ne a ranar 3 ga watan June Shekara ta 1989 a lissafin watannin Miladiyya, Wanda yayi dai-dai da ranar 28 ga watan Shawwal shekara ta 1409 a lissafin watannin Hijiriyyah.
Imam Ayatollah Al-Qhumaini (Qs) shine jagoran da ya jagoranci kifar da haramtacciyar Gwamnatin Sarki Shaa na kafirci a Ranar 1 ga watan February 1979 bayan ya dawo daga kasar France sakamakon korar da Sarki Shaa yayi masa na tsawon lokaci, Wanda wannan juyin juya halin shine yake cigaba da gudana sama da Shekaru 40 kenan a kasar ta Iran.
Imam Khumaini (Qs) yayi wafati ne sakamakon rashin lafiya da yayi fama da shi na wasu lokuta. Inda a wannan lokacin duk da matsanancin rashin lafiya da Imam (Qs) yake fama da shi bai hana shi gabatar da Ibadoji ba (Sallah) tun yana yi da kansa har ya kai ga sai an rike shi yake iya yin Sallar, har Allah ya karbi ransa a wannan rana ta 3 ga watan June na shekarar 1989.
A yau din ne kuma taron Makon Imam Khumain (QS) din zai fara gudana a kasar Iran kaman yanda aka saba duk shekara. A wannan Shekarar sakamakon yanayi na Annobar Covid-19 da ake ciki a fadin Duniya, za a gabatar da taron ne a cikin Talabijin, wanda Jagora Sayyid Ali Khamne'i zai gabatar da jawabi insha Allah. Muna fatan Allah ya qara Jaddada Rahama a makwancin Imam (QS) ya kwato mana Jagoranmu Sayyid Zakzaky (H) a hannun miyagun Azzaluman kasar nan ya cika ma Jagoranmu burinsa na tabbatar addini a wannan Nahiya da ma Duniya baki daya.
Daga Walikan Mu Na Saminaka
Tare Da
- Ibrahim Almustapha Saminaka
- 3/June/2020
Tags:
Munasabobi
