Gugu-gugun ɗaliban Jami'a ne, suke Zanga-zanga, a gaban Ofishin Jaladancin Swiss, dake babban birnin Tehran, na Kasae Iran game da kisan da Americawa suka yiwa wani baƙin fata mai Suna George Floyd, a hanun wasu fararen Turawa a ranar 3 ga watan Yuni, 2020.
Ɗaliban sun hadu a wajen Ofishin Swiss, ofishi dake wakiltar Washington a ƙasar iran din a ranar Laraba da yamma domin nuna fushin su, da kin amincewa da wannan zalunci da US keyi wanda hakan ya saɓawa doka da da tsarin Ƴan adamtaka.
Abin bai tsaya nan ba, har ɗalibai wadanda ba ƴan kasar ba suma sun bi sahun wannan zanga-zanga a Babban birnin na Tehran.
Masu zanga-zangar sun fito ne dauke da hotunan baƙin fatar da da faɗin yadda abin ya faru cikin fastoci.
Suna cewa, "Floyd bakin fata dan America da baida ko makami, ƴan sanda fararen fata (Minneapolis) sun kayar dashi ƙasa, a ranar 25. Dan sanda daya daga cikin su ya saka guiwar kafar sa a wuyar Floyd wajen tsawon minti goma (10) har takai Floyd yana cewa, "Bana iya numfashi" (I can't Breathe".
Foreign minister na Iran yayi magana mai ƙarfi akan kisan da ake wa baƙaƙen African-American a United State, da halin da ke faruwa bayan kashe George Floyd na zanga-zanga.
"iran tayi Allah wadai da kisan baƙaken fata, da ci gaba da kisan a America, ta kuma kirayi masu iko (Authority) dasu gaggauta yin adalci akan ko wani matsala" Fadar Ministan a Shafin sa Na twitter.
Daga Wakilan mu na Saminaka
Tare da Bin Haroun Sigau
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya
