Kalmar Ridda Ba Tana Nufin Barin Muslunci Bane, A'a, Saɓa Umurni Ne!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

BAN GA TA YADDA ZA KA CIRE MUNAFUKAI DAGA CIKIN SAHABBAI BA

A matsayina na musulmi wanda ke yin sallah da azumi , kuma mai shaidawa da LAA ILAHA ILLAL-LAH MUHAMMADAR-RASULUL-LAH ba za a kashe ni kawai don na qi bayar da zakkar dukiyata ba, sai dai a sanya ni cikin masu saba umarnin Allah .

Shi kuma munafuki ana samunsa ne cikin musulmi wanda ya furta kalmar shahada amma yana son kafirci da kafirai cikin zuciyarsa tare da yiwa muslimci zagon qasa.

Duk wanda ya rayu tare da Annabi (S.A.W.W )kuma yayi imani da shi cewa dan saqo ne daga Allah , to, shi sahabi ne komai munin aikinsa, sai dai kawai ka kira shi ba mumini bane.

Sunan da Annabi (S )ya sansu da shi kenan sahabbai , sai dai kawai masu tawili suyi tawilinsu .

(1)- Abu Huraira ya bada labari cewa, Manzon Allah (S.A.W.W )yace;

‘’ Wasu jama'a daga sahabbaina za su nufe ni ranar alqiyama , sai a tsare su daga Tafkina, sai nace;Yaa Ubangiji, Sahabbaina ne! Sai ace;

‘’ AI BA KA SAN ABINDA SUKA AIKATA A BAYANKA BA, LALLE SUNYI RIDDA AKAN DUGADUGANSU BAYA-BAYA .‘’

(Bukhari , hadisi na 6585).

(2)- Daga Abu Huraira, daga Annabi (S.A.W.W ) yace;

‘’ Ina nan (tsaye )ranar alqiyama sai ga wasu jama'a, har sai na gane su (wane da wane da wane ne )sai wani mutum ya fito tsakanina da tsakaninsu yace;‘’ KUZO NAN !‘’

Sai nace, zuwa ina?Sai yace, ‘’ WALLAHI ZUWA WUTA !‘’ Nace, menene labarinsu?yace, ‘’ AI SUNYI RIDDA NE A BAYANKA KUSA-KUSA .‘’

Sa'an nan sai ga wata jama'a har sai na gane su (wane da wane ne )sai wani mutum ya fito tsakanina da su yace, ‘’ KUZO NAN !‘’ Nace, zuwa ina ?Yace, ‘’ WALLAHI ZUWA WUTA !‘’ Nace, menene labarin su? Yace, ‘’ AI SUNYI RIDDA NE A BAYANKA KUSA-KUSA !‘’

Ba zan daina ganin yana kebewa dasu (zuwa wuta ba sai 'yan kadan )(MISLU HAMALIL-NI'AMI ).‘’

(Bukhari , hadisi me lamba 6587)

To, ban dai san me za kuce kan wadannan hadisan Bukhari ba .

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~1st June, 2020/ 11-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post