@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
YANZU MUSLIMCI YA ZAMA KAYAN ADO (fashion dress )
Wannan abu na matuqar damuna cikin zuciyata , wani lokaci in na zauna sai na ji kamar nayi kuka, amma sai naga yin kukan ma ba zai amfanar dani ba.
70% na musulmi sun shiga rigar muslimci ne, amma babu ruhin muslimci a gangar jikinsu . Sun riqe shi ne kawai a matsayin kayan ado (fashion dress )wanda idan mutum ya sanya shi a jikinsa zai zama abin kallo .
Sam, wannan ba shine ma'anar muslimci da koyarwarsa ba, domin muslimci na koyar damu ne qaunar juna, tausayi, taimako da kuma nisantar abinda Allah ya hane mu aikatawa, amma in ka kalli mafi yawan musulmi sai kaga babu wannan tare dasu.
Ya zo cikin hadisi inda Annabi (S.A.W.W )ke cewa;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ Shi mumini a wajen mumini tamkar gini (building )ne, sashensa na qarfafar sashe .‘’
- Bukhari , J:1, SH:129.
- Muslim , J:8, SH:20.
A wata riwayar kuma yake cewa;
‘’ Misalin muminai wajen qaunar junansu da tausayin junansu, kamar gangar jiki ne guda daya, duk lokacin da wani bangare (na jikinsa )ya koka sai sauran dukkan jiki ya dau radadi (pain )da rashin bacci .‘’
- Bukhari , J:8, SH:91.
- Muslim , J:8, SH:20.
Wadannan hadisai na fassara ayar nan ne da ke cewa;
‘’ KUMA MUMINAI MAZA DA MUMINAI MATA SASHENSU MASOYI NE GA SASHE .....‘’
(TAUBA, AYA TA 71)
Sai dai mu ba haka muke ba, maimakon ka samu musulmi na tausayawa abinda ya sami dan'uwansa sai ka ji yana cewa madalla .
Akwai yiwuwar wani yace ai su wane ba musulmi bane ko ba muminai bane, sai dai kuma sai ka samu cikin masu da'awar cewa sune muminai ne suna cin amanar junansu da yiwa juna hassada ko qyashi .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~1st June, 2020/ 11-10-1441.
Tags:
Tunatarwa


