Uba shine tubalin ginin gida har ya zama an sami iyalai na gari, Lalacewar tarbiyyar iyali takan faro ne daga Mai gida, ita mace mai bi ce in har Ka gyaru, ka kuma nemi a gyara sai gyara ya tabbata, amma a n Mai gida ya lalace, to bada shi kadai ne ya lalace ba, dukkan iyalin ne.
Zamanin nan da muke ciki yana tasiri ga Lalacewar tarbiyyar mu, ƴan uwa mun koma kamar amawa, kai zan iya cewa yanzu tafiyar da ake na rashin jagora a cikin mu ya saka muna nema mu zarce amawa wajen shagalin da kaucewa gurbata da aka ɗora mu.
Abin zai baka mamaki, In Ka kalli halin da muke ciki, sai ka ɗauka dama ce muna yiwa Malam ne ibadun da muke da kuma, kusan tare Allah da muke Tata yi. Amma yanzu tafiyar ta fara sauya zabi, mazajen mun lalace, balle kuma akai ga matayen mu.
Yanzu a kai matsalar da Sister inda abin ka shiga gidan da suke rayuwa ne, wallahi innhar kai mai kishin addini ne saboda ka kusan zuba hawaye. Sabida taɓarɓare War lamarin, sam mun zubar da ginin da su Malam (H) suke ta kokarin yi mana, Sisto sun zama zabiyoyi, wajen iya rera wakokin waɗannan shagalallun zamanin.
Ina abin ka tara wayoyin su ne, sai ka jima baka sami wanda take da tafsir ɗin malam ba, daga waƙoƙin ƴan hausa sai waƙoƙi shikenen, In kuma yaro yasan yi wani kuskure maimakon a jawo shi jiki, a nuna masa rashin kyawun abinda ya aikata, a'a yanzu kaje ana kututtubo mishi ashar. Anya tafiyar nan za'a yi ta damu kuwa??
Kullum burin Sayyid mu gyaru, amma kuma sai ƙara taɓarɓare wa muke, samari ƴan Mata su kuma basa da aikin yi sai yawan yaudarar juna, da karairaku, kai kace ba addini ne hadafin mu ba. Shawara ta anan shine lallai, mu lizimci sauraron jawabin jagora, kamar Tafsir, da sauran munasabobi, groups-groups suna da yawa na yada tafsirin Jagora Da wakilan da'irori.
Ina muka riki wadannan zamu fita cikin Ruɗi n da muke na rashin jagora a tare damu, kar mu bawa maƙiya damar da suka jima suna nema akan mu don cimma muradun su. Kar yazama abinda da suke nema ya ƙarfi da yaji yanzun muna basu a kyauta, In mukami haka zai zamana mu kanmu shaidanu ne basai sun Turi wani shaidan don ya lalata mu ba.
Don maƙiyan addinin nan sun gane, da lalata tarbiyyar mu ne kawai zasu iya galaba akan mu, shiyasa kullum neman hanyar da zasu shiga jikkunan mu suke, sigar ayyukan mu ya zama daidai da muradun su. Shikenen haƙar su ta cimma ruwa. Sai su bari da kan mu, domin sun hana da lahirar mu, su tarayyar imani suke, taya zamu basu dama??
Mu kiyaye mu kula, a ƙalla ya zama in aka karbi wayar dan uwa/ƴar uwa ya zama karatu, wa'azi sufi komi yawa, kai har ƙasidu ma ya kamata a rage sauraron su, don karatuttukan sune aula fiye dasu. Yanzun sauka jima baka wata sister a dakin mijin ta ta kunna jawabin jagora tana sauraren ba, sai waƙoƙi.
Wannan abin takaici ne gare mu, In ko aka dauko bangaren daka hijabi, ba'a cewa komi domin, dama da yaqar sistocin mu sabida zuwa wajen program suke saka hijabi, koda a gidan yawa ne yanzu ka shiga bazai iya bambance sister da sama ba, sabida shigan da sistoci keyi yafi na aamawa taɓarbare wa.
Allah ya sayar damu, ya kuma tsayar da dugadugan mu kan tafarkin addin, ya ƙare mu daga santsin addini, ya kuma azurta mu da zuriya ta gari. Ya Allah ga bawan ka nan a hannun azzalumai bashi da gata In bakwai ba, ka kwato mana Su Sayyid Zakzaky (H) cikin koshin lafiya, ka ƙara musu nisan kwana alfarmar Imam Hussain (A.S).
Daga wakilan mu Na Saminaka
Tare da
Bin Haroun Sigau
08065008793
Tags:
Tunatarwa
