Misalin Sayyid (H) A Wannan Zamani Tamkar Annabi (S.A.W.W) Ne A Zamanin Sa!!!




@ MA'ASUMAH NIGERAN NEWS UPDATED @

Aikin mutum ne ke fassara shi wanene ko kuma ya jingina shi da wani mai aiki irin nasa .

Idan muka bibiyi tahirin Misra ta Dauri za muga cewa duk wanda yayi mulki a cikinta ana kiransa Fir'auna ne sakamakon kamanceciniyar aikinsu, amma ba shine asalin Fir'aunan da yayi zamani da Musa (A.S )ba.

Manzon Allah (S.A.W.W )ya misalta Imam Ali (A.S )da Harunan Musa (A.S), amma ba yana nuna cewa shima Annabi ne kamar Annabi Haruna (A.S )ba, sai dai ya danganta misalinsu ne da irin aikinsu .

Aikin da Annabi (S.A.W.W )yayi cikin sahabbansa shine qoqarin tunkude su daga shiga wuta ta hanyar jawo su cikin shiriya da bin dokar Allah , amma a haka suka riqa fisgewa zuwa fadawa cikin wuta .

Riwaya daga Abu H uraira , daga Annabi (S.A.W.W )yace;

‘’ Misalina da misalinku kamar misalin mutumin da ya kunna wuta ne, yayin da (wutar )ta haskaka (dukkan )abinda ke gefenta, sai ga fari da wadannan dabbobi da ke fadawa cikin wuta suna ta fadawa cikinta. Shi kuma (mutumin )yana ta qoqarin tare su, su kuma suna galaba a kansa (ta hanyar kangarewa )suna fadawa cikinta .‘’

Yace,

‘’ To, wannan shine misalina da misalinku, ni ina riqe madaurin wandonku (don kada ku fada )wuta , ku kuma kuna rinjayata kuna fadawa cikinta .‘’

-Bukhari , J:8, SH:127

-Muslim , J:7, SH:63.

Kamar hakane Sayyid Zakzaky (H )ke nuna muku cewa konsitushan wuta zai kaiku, ku kuma kuna yaqarsa cewa sai kun fada cikin wannan wuta .

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

Talata, 9th June, 2020/ 19-10-1441.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post