@ MA'ASUMAH NIGERAN NEWS UPDATED @
DUK TA INDA GASKIYA TA FITO KARBARTA AKE YI
Shi matsayi ana samunsa ne ta hanyar sallama al'amari ga Allah cikin ayyukan da zantuka, dangantakarka ga Annabi ba za ta taba zama hujja ba matuqar aikinka ya bambanta da nasa.
Ba bisa son rai bane Allah ya fifita 'ya'yan Sayyidah Fatimah akan sauran 'ya'yan Imam Ali (A.S )ba, kuma ya fifita 'ya'yan Imam Hussaini (A.S )da Imamanci kan 'ya'yan Imam Hassan(A.S )daga cikin 'ya'yan Fatimah (S.A )ba.
Ga dukkan ma'abota wilaya kuma masu karatu sun san da wannan ba tare da neman qarin bayani ko sharhi ba. Kamar haka abin yake cikin waliyyai da mujaddadai.
Allah (T )bai halakar da dan Annabi Nuhu (A.S )don tozarci ko nuna gazawar Annabi Nuhu (A.S )bane, kuma bai zargi 'ya'yan Annabi Ya'aqub (A.S )kan abinda suka yiwa dan'uwansu Yusuf (A.S )don muzantasu bane, a'a, yayi haka ne don ya zama ma'auni na tantance gaskiya da qarya ko gane wanda ke kan shiriya da wanda ya kaucewa hanya .
Saboda haka kasancewarka dan Annabi ba zai taba zama hujja nayi maka biyayya ba matuqar ka saba koyarwarsa, amma haqqi ne abin tambaya ga muminai idan suka saba maka ciki abinda ka kirasu akai matuqar bai yi hannun riga da dokar Allah ko koyarwar da'awar muslimci ba.
Saboda haka a kullum ana duba inda gaskiya ke fitowa ne ba tare da la'akarin da cewa shi wanene ba.
ALLAH YA FAHINTAR DAMU GASKIYA DA BIN TA .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
Talata, 9th June, 2020/ 18-10-1441.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar ilimi