Matsayin Kashe Rai A Wurin Shi'a





"Don ka sani duk wani mutumin da ake ce mishi Shi'a, in dai shi Shi'iy din ne, to ba yadda za a yi ya je ya kashe mutum. Saboda kisa ko da na shari'a ne (wanda shari'a ta yarda) a wajenmu sai Mujtahidi (wanda ake ce ma Ayatullah) shi zai ba da fatawar a yi sa. To kuma a iyakan saninmu duk fadin Nijeriya ba Mujtahidi ko kwara daya.

"Wato in ta kai ma ga za a hori mutum har jini ya fito, ko ba za a kashe shi ba, Ittifakan a Mazhabar Shi'a ba Wanda yake da ikon ya yi wannan sai Mujtahidi. Wannan ko da Ba kisa bane. To ta ina ne za Ka yi tunanin wani Shi'a zai kashe wani?

"Ko da suka kirkiro su Alka'ida da sauransu suka ce 'Yan Ta'adda, ai ba su taba tunanin su kirkiro wata suce wadannan 'yan Shi'a bane. Basu da na Shi'a ko guda daya, tunda sun San cewa ba zai yiwu wani Shi'i ya je ya yi kisan kai ba, saboda sai da izinin Mujtahidi. Kuma ba zai yiwu su samu Mujtahidi ya zama Dan Ta'adda ba, ba kuma za su iya kirkiro Mujtahidi ba.

"Saboda haka ko da suke yayin yan ta'adda, in ka lura ko a tarihi ba Dan ta'adda Shi'a Sam! Ko da wai ba za Ka taba tsammanin wani Shi'i zai kashe wani ba.

"Wannan kisa bisa shari'a muke nufi, ballantana kuma ka je ka kashe wani haka kawai sunanshi kisan kai. Wanda Allah (T) yake cewa: "Wanda duk ya kashe Mumini da gangan, sakamakonsa Jahannama, kuma Allah ya yi fushi da shi, ya tsine masa, ya yi masa tanajin babban azaba."

— Sheikh Ibraheem #Zakzaky @Yaumus Shuhada 2012.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post