Anya Kuwa Ƴan Shi'a Zasu Amfane Mu A Najeriya??




_A baya dai ni nasan akan kirasu da masu kishin Addini sabida yadda suke gwagwarmaya sosai ko kuma acedalibai, a lokacin ban mancewa akwai su Sunusi Lamido Sunusi na 2, da su Sheikh Turi, kafin daga baya naga kamar an Shi'antar da gwagwarmayar gaba daya tun dawowar Zakzaky daga Iran 🇮🇷 bayan Khumaini yayi juyin juya halo wato Revolution._ *_Sai ya zama na waje baya sha'awar gwagwarmayar sabida Salafawa sun sami abin fada, su kuma ''yan shia suka ja baki sukai shiru._*

      _Bana mantawa, 'yan Jarida sun taba tambayar Zakzaky cewa koshi dan Shi'ar ne? Sai yace "yadda nake a baya haka nake ban canza ba, iya abinda na sani shine ni musulmi ne kuma musulunci nakeyi. Idan ka daukeni shi'a ka tafi a haka, idan ka dauke ni sunna ma ka tafi a haka" ina tsammanin haka kalaman suke._

*_Ni na karanci Sociology ne, kuma nakan bibiyi jawaban Al-Zakzakin Zaria a taron Sha'aban da taron Shahidai. A gaskiyar ba gwamnati bazata barshi ba, dole zatayi penetrating alamjiransa da Spies jami'ai da daman gaske, a lokaci guda gaskiyar magana be mori almajirai ba wayayyu da zasu iya facing wannan challenge din ba. Kuyi hakuri, fadace fadacen cikin ku kawai ya isa ya hanaku cigaba._*

      _A tunani na fatan gyaruwar kasar nan yana hannun ku ne, amma 'yan Shi'ar dacan baya lallai ba su bane na yanzu tun a dabi'a da halaye zaka banbance, nasan kun sani, na Yanxu sun zama matsorata marasa tarbiyyah yaransu da manya, sabida ina cikin su._

     *_Ku fahimci wani abu masu karatu; wannan malamin ya samar wa da almajiransa sectors da zasu cigabantar dasu wadda ko federal government bata da su, kuma wallahi kaf malaman kasanmu ba wanda zai iya._*

. _Zakzaky ya samar da wasu ana kiransu 'yan Isma, masu harkar kiwon lafiya, ya fada masu cewa nan gaba asibitocin Nigeria zasu lalace ku zaku amfani 'yan kasar nan, ni naji lakcar sa abokina dan shi'a ya fada min, amma a zahirin gaskiya su kansu 'yan Shi'ar basu anfana da iya su kuma masu aiki basu muhimmantar ba._

     *_Ya samar da 'yan Shuhada ake cewa ko Mu'assasa? Masu kula da marayu, amma 'ya'yan abokina dan shi'an da aka kashe gasunan a wahale na abinci ma sai anyi da kyar balle suyi maganar taimakon gama garin Al'ummar kasar gaba daya._*

. _Na tabbata da suna taimakon marayun yaran da ''yan boko haram suke kashewa, da yanzu kaf ''yan Borno, Yobe, Zamfara da sun zama shi'a._
. *_Zakzaky ya samar masu da Media masu karfi masu suna IM Publication da Almizan, bana mantawa, yaron sa ke kula da media ta bangaren social media da yada jawaban Zakzakin wadda ta sanadiyyarsa muka ma fahimci waye Zakzaky a hakikan shi ba rumors din makiyansa ba. amma bayan kashe yaro almajirai Million 25 sun kasa samun standard mutum 10 da zasu iya tafiyar da media into kodama Domestic Bawai International standard ba, balle kuma azo kan Almizan, lalacewar kam ba'a magana, don ta zama jaridar maxhaba. Koran da Zakzakin yakeyi kuwa ina da tabbacin bana maxhaba bane_*
. _Ta bangaren dalibai 'yan Academic forum kuwa, tasirin su bema kai kaso 30℅ cikin 100℅ na yadda Zakzaky yayi a lokacin da yake makaranta ba._
. *_Zakxaki ya shirya taimakon al'ummar najeria amma gaskiya a fahimtana mabiyansa ne basu shirya ba._*

. _Idan kuwa muka dawo bangaren taimakon al'umma, ba kamar da ba, domin kuwa wasu 'yan shi'an a anguwan mu dasu ake satan kayan mutane, kuyi hakuri, kamata yayi ku gyara._

. *_A gaskiyan magana, nayi niyyar shiga shi'a, amma na gane gwara na xama almajirin Zakzakin kawai, sabida nasan shi kuma na nazarce shi mutum ne na musamman da yasan zamanin sa da addinin sa._*

. _Amma a gaskiya indai gwagwarmaya ce ta Zakzaky, tofa babu ita yanzu domin kuwa mutanen mu Sociologist sun ruguza ta sabida na san su sarai zasu iya, muddin 'yan shi'ar basu bi maganar malamin nasu ba wayayye su gane hadarin su ga yahudawa ba._
. *_Shiyasa nace; anya kuwa ''yan shia suna da amfani kuma zasu amfane mu?_*

. _Fatana Allah ta'ala ya barni da Zakzaky don ni na zama almajirin sa kawai, "uhm._
. *_Kuma ya bude mana idanu mu fahimci gaskiya, ya bamu ilimi me amfani, inda nail kuskure ku have min idan abin yai maku ciwo pls. _*
_Kuma yasa muga Annabi Muhammadu sallallahu alaihi wa sallam._
Bis-salam ku huta lafiya

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post