Matan Wakilan Harka Islamiyya, Ya Kamata Sufi Ko Wacce Sister Tarbiyya!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

ZAMANTAKEWAR WASU MATAN ANNABAWA (A.S )BAI AMFANAR DASU KOMAI BA 

Idan muka ce wakilan harka muna nufin dukkan wani dan'uwan da Allah ya zabe shi don ya wakilci 'yan'uwa kan da'awar Sayyid (H ), ko da kuwa su 2 ne a garinsu .

Ba za ki taba zama abin koyi ga matan kirki ba har sai kin kasance ta kirki cikin dukkan mu'amalat naki da jama'a, musamman zamantakewarki da mijinki.

Idan kika sami kanki cikin daya daga matan wakilan harka islamiyyah sai ki qara godewa Allah , domin ya qara yi miki baiwa ce kan wacce kike da ita.

Darajar miji kan shafi mace matuqar mijin nata mai daraja ne, domin a kanga girmanta da darajarta albarkacin mijinta, kuma takan zama cikin masu fada a ji cikin 'yan'uwa mata.

Saboda haka wajibi ne a kanku ku kasance masu mutunta harka ta hanyar kyautata dabi'unku, rashin kyautata dabi'a ko tarbiyyarku kan zama illa cikin harka , domin wasu za su iya yin koyi daku ko kuma ba da misali daku .

Ko da ba ki da ilimin da za a dora ki kan 'yan'uwa don yi musu jawabi, idan kin kasance ta kirki za a riqa ganin girmanki da daukar maganarki .

Sai dai wani abin takaici shine , ko da ace mace ita kadai ce wajen mijinta sai ka tarar ba ta aikata abinda ya kamata ta aikata ga mijinta . Idan kuma sun kai su biyu sai ka tarar ana samun sabani a tsakaninsu maimakon su kasance masu hada kansu don su zama abin koyi ga wasu .

Ta yadda ba zai zama abin mamaki ba shine, yadda aka sami wasu matan ANNABAWA (A.S ), wadanda zamantakewarsu bai amfanar dasu komai ba.

Allah (T )ya bada misali ga matar Nuhu da matar Lut (A.S )don su zama darasi ga mata. Aka ce musu,

‘’ KU SHIGA WUTA TARE DA MASU SHIGA .‘’

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

          09039791509

Litinin, 8th June, 2020/ 18-8-1441.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post