Wai Da Gaske Ana Ci Gaba Da Tsare Shugaban Ƴan Shi'a Ne Bisa Ganin Damar Su???




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

DA KUN CE MIN HAKA HANYAR TAKE ZAN FI GASKATA KU

'Yan shi'ah dai sun fada cikin wata matsananciyar jarrabawa wacce babu wanda ya taba fadawa cikin irinta a tarihin wannan qasa Nigeria . Tun ana murna da abinda ya faru a kansu sakamakon abinda ake cewa shi ya janyo musu, yanzu 50% na masu murna sun dawo tausaya musu.

Ina daga cikin masu tausaya musu, amma sai ina cin karo da wasu maganganun da ke fitowa daga bakunan wasunsu na cewa wai ganin damarsu ce tasa ake cigaba da tsare jagoran nasu, wai da sunga dama kuma sun shirya da tuntuni an sako musu shi .

Wannan magana tana daure min kai, domin a tunanina da fahintata suna aikata dukkan abinda ya kamata su aikata wanda wasunsu ba za su iya aikatawa ba in da irin hakan a kansu ta auku.

Suna zanga-zanga ana kashe su ba su fasa ba, suna addu'o'i, wa'azozi tare da rubuce-rubuce a social media , amma a haka suna zargin junansu cewa wai ba suga dama bane da an sako shi.

        TAMBAYA

(1)- Ashe dama ganin damarku ce tasa aka aikata abinda aka aikata a kanku da jagoran naku?

Tabbas , maganganunku sunyi kama da haka.

(2)- A tunaninku me za ku aikata wanda yafi wanda kuke yi a yanzu?

Da kunnena na ji sheikh Zakzaky na cewa, duk wanda ya kama hanyar gaskiya dole irin abinda ya sami magabata ya same shi , kuma ma na ji daga bakunan wasu maluma koma bayansa .

GASKIYA DA CEWA KU KAYI HAKA HANYAR TAKE ZAN FI GASKATA KU FIYE DA WANNAN MAGANA TAKU.

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda .

          09039791509

Litinin, 8th June, 2020/ 18-10-1441

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post