@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
DA BA DON WANNAN AKE DUBAWA BA, TO, DA WASU SUN CI BULUS
Allah gwanin hikima da sanya komai nasa inda ya dace, ya san abinda kowa zai aikata a farkonsa da qarshensa.
'Yan Adam halitta ce wacce Allah yayi kuma ya fifitata kan kowacce halitta tare da rarraba tunanin kowa yasha bamban da juna . Wasu tunaninsu na da kaifi ta yadda za su iya gano hikimar Allah cikin sauqi ko da kuwa ba ayi musu sharhi ba, wasu kuma ko kayi musu ba sa fahinta .
Wasu kan kalli mutum ne su fassara shi kan abinda ya rayu s kansa ba wai akan me ya cika ba, irin wannan tunani kuwa ya sabawa hankali da shari'a , domin akwai wadanda suka rayu cikin kafirci kuma suka cika da imani , wasu kuma suka sami yabo daga Annabi (S.A.W.W )amma suka canza a bayansa.
Imam Ahmad yace, Yazeed ya bamu labari , Humaid ya bamu labari daga Anas cewa Manzon Allah (S.A.W.W )yace;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ Ba naku bane yin mamakin (aikin )dayanku har sai kunga akan me zai cika, domin mai aiki zai iya aiki zamani guda daga rayuwarsa ko akan shiriya daga qarni yana aikata kyawawan aiki wanda da zai mutu a kansu zai shiga Aljannah , sa'an nan sai ya canza ya aikata mummunan aiki.
Kuma bawa zai iya aikata aiki na muni
qarni guda, da zai mutu a kansa da wuta zai shiga, sa'an nan sai ya canza ya aikata kyakkyawa. Idan Allah ya nufi bawansa da alkhairi sai ya ba shi aiki kafin mutuwarsa .‘’
Suka ce, yaa Ma'aikin Allah , ta yaya zai ba shi aiki ?Yace,
‘’ Sai ya datar da shi wajen aikata kyakkyawa, sa'an nan ya karbi ransa a kansa.‘’
(Musnad Ahmad, J:3, SH:120)
Wannan abu a fili yake, domin an sami wadanda suka muslimta a filin yaqi suka sami shahada, wasu kuma suka rayu cikin muslimci suka canza a bayan Annabi (S.A.W.W ).
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~31st May, 2020/ 10-10-1441.
KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
