Part (¡¡)
✍️Auwal M Tukur
5/6/2020
Hanyoyin da suke karfafa dankon zununci a al'umma,su ne wadanda aka ginasu a kan asasin tausasawa da soyayya ta gaskiya. Shakuwar zukata ita ce take kawo hadin Kai da kaunar juna mai zurfin gaske. Saboda haka babu makawa mutum yayi watsi da sabanin da ke tsakaninsa da wasu domin kulla abuta ta gaskiya, sa'an nan kuma ya yarda da gaskiyar da 'yan'uwa suke kiran sa suwa gare ta. Abuta ta gaskiya ita ce wadda ba a kulla ta saboda abin hannun juna ba,kuma ta kasance cudanya da ruhin 'yan'uwataka wanda zai gamsar da zuciyar dan Adam mai bukatar soyyaya. Duk wani aboki na gaske to wajibi ne ya guji raunana jigon abuta a zuciyarsa ko ta halin kaka. Sannan ya yi kokarin yaye wa abokin nasa kuncin rayuwa da yan mamaye zuciyarsa,kuma ya shuka masa fata nagari da natsuwa a zuciya. Bai kamata mutum ya yi abuta da kowa ba ko ya ishisshire a inuwarsa,sai ya tabbata zuciyarsa a cike take da sonsa da kaunarsa. Wani masani yana cewa:
```"Rayuwarmu kamar kogon dutse ce,duk yayin da mutum ya kwalla kira sai ya ji amon muryarsa. Saboda haka duk wanda zuciyarsa take da soyayya ga sauran jama'a ba zai ga kome daga gare su ba illa soyyaya. Harkokinmu na duniya duk cude-ni-in-cude-ka ne, amma ba wai muna nufin mu ce al'amarummu na ibada ma bisa wannan asasin aka tsai da su ba. Amma ta yaya zai halasta a gare ka ka so wasu su kyautata maka alhali kai ba ka kyautata musu ba? Kuma ta yaya za ka nemi soyayya madawwamiya daga gare su alhali kai ba ka dawwama a kan soyayyarka gare su ba?```
Zamu ci gaba...

Tags:
Daga marubata