Part(3)

✍️ Auwal M Tukur
6/6/2020
Zaman taren da babu kaunar juna da igiyar soyayyar da ta daure zukata, ba zai haifar da kome ba face dacin rayuwa da azaba.
Idan riya ta yi kanta a zukata da rayuwar mutane,kuma bambadanci domin neman abin duniya ya maye gurbin abuta da zaman tare,to sai kyautata was juna da zaman tare su yi rauni Kuma a rasa taimakekeniyar a al'umma.
Ba shakka,a rayuwarku,kun taba yin ido hudu da wasu mutanen da babu kauna da rahama a zukatansu. Amma sun yi shigar bultu,sun sanya tufafin abuta, kuma sau da yawa ba za ku iya gane gaskiyar al'amarinsu da aibobin da ke tattare da su ba,don haka kwaskwarimarsu take rinjayar ku zuwa gare su.
Days daga cikin sharudan alheri da tafarkin tarbiyyar ruhi,ita ce kulla abuta ta gaskiya da salihan mutane. Saboda zuciyar mutum kan sami tarbiyya a sakamakon zama da su,ruhinsa kuma ya daukaka daga matsayinsa na al'ada zuwa ga matsayin takawa da falala. Saboda haka ya wajaba akan mutum ya yi kyakkyawan tunani wajen zaben abokai. Kuskure ne mutum ya yi abuta da Wanda bai yarda da shi ba. Domin shi mutum an halicce shi da daukar halin wanda yake tare da shi yau da kullum. Kuma wannan shi ne abin da ake tsorace wa sa'adar mutum, kada ya fandarar da ita ya tozarta.
*WANNAN DAI TUNATARWACE ALLAH YASA MU AMFANA*

Tags:
Daga marubata