Kimar Abota... Part 1

Part(¡)

✍️Auwal M Tukur
         4/6/2020

Kauna tana daya daga cikin dabi'un mutum, saboda haka ne muke ganin zuciyar mutum tana ingiza shi zuwa ga shakuwa da wasu daga cikin mutane. Ba zai yiwu a  dankwafe Wannan dabi'a ba. Dan haka yake zama wajibi a biya wa zuciya wannan bukatar. Kowa yana kulla abuta ne da wasu makamantansa a cikin jama'a domin ya zauna tare da su ya debe haso.

  Abuta tushen aminci da natsuwa ce, kuma tana daya daga cikin abubuwa masu ba da kwanciyar hankali. A duk fadin duniyar nan babu wani abu da ya Kama kafarya a kima.

  Kuncin kadaitaka da rashin aboki yana daga cikin masifu masu tsanani. Idan ba domin soyayya ta hada mu da juna har zukatanmu suka shaku da ta juna ba, to da bakin cikin da damuwa sun yi wasan kura da mu, duniya kuma da ta zame mana baka kirin. Wani masani yana cewa:
    "sirrin alheri shi ne alakarmu ta kasance ta yan'uwantaka ba ta kiyayya ba, domin duk wanda ba zai iya son mutane  'yan'uwansa ba, to a bisa dabi'a ba zai rabu da kunci da damuwa a rayuwaba.

Zamu ci gaba...

1 Comments


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post