In ma har baza ka bi doka ba to baza ka qi bi da sunan Shi'a ba, ba sunan ka Shi'a bane, sunan ka wanda yaqi bin doka na wawayen gari – Sheikh Zakzaky (H)



A WANI JAWABI NA SHEIKH ZAKZAKY YAKE CEWA

 " In ma har baza ka bi doka ba to baza ka qi bi da sunan Shi'a ba, ba sunan ka Shi'a bane, sunan ka wanda yaqi bin doka na wawayen gari. Ba sunan ka Shi'a bane, su wawayen da suka yi doka tsaban wauta ne wannan, ba doka tasa mutane suke hawa babur ba talauci ne da wahala, tilas ta sa su, saboda haka ba doka za ayi a hana su ba, za a samar musu da yanayi ne da baza su bukaci babur din ba. Me yasa mutane suke hawa babur a matsayin haya? Tilas da chan akwai ana hawa babur ne ayi haya? Wa yasan ma za a hau babur ayi haya dashi.

 Saboda haka idan kuka samar da yanayi da baza a bukaci babur ba, baza a ma ga babur ana haya dashi ba. Kuma sai suka zo suka ce ba wai sun hana haya ne da babur ba sun hana goyo ne. Ma'ana koda naka ne na kan ka zaka hau, baza ka goya wani ba, to wannan ne tsabar rashin hikima. Har ma ance wani kwamishina yace ko matar mutum ne ko zai kai ta asibiti ne bazai goya ba, ma'ana ko zata mutu ne bazai goya ba. Haba Mista kwamishina".

 - Jawabin Sheikh Ibraheem Yaqoub Al-Zakzaky (H) a lokacin da aka hana goyo a kan babur (Mashin)
 - Ibrahim Almustapha Saminaka ya Naqalto muku.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post