Iyali A Muslunci Fita Na Biyar (5)... Ladubban Daren Farko Ga Sabbin Ma'aurata




Yazo a ruwaya daga Manzon Allah (S) yace wa Imam Ali (A.S), "Bayan Amarya ta shiga ɗakin ka, ta zauna, ka cire takalmin ta ka wanke kafarta, ka kuma zuba ruwa daga wajen daka wanke mata kafar zuwa ƙuryar ɗaki.

Idan kayi haka Allah (T) zai ɗebe nau'ikan talauci guda saba'in (70) daga cikin gidan ka, zai kuma shigar da nau'ikan arzuƙa guda saba'in (70), da albarka saba'in (70), kuma Allah zai ta aiko da rahama gare ku har guda saba'in, su rufe kan amaryar ka har sai ko wanne kusurwar gidan ka ya cika da albarkoki.

Idan kuka aikata haka, amaryar zata kasance cikin kariya daga cututtuka, da cutar hauka matuqar tana a wannan gida (Gidan ka)." An kuma ruwaito cikin Hadisan Ahlul Bayt (A.S) cewa, "Mustahabi ne ga sabbin aure suyi sallah Raka'a biyu (2) daga cikin Salloli 58, kuma bayan sallar sai ayi Godiya da yin Salati ga Manzon Allah da iyalan gidan sa sannan a yi wannan Addu'ar:

Allahummar-Zuqni Ulfaha wa wuddaha wa ridhaha be; wa-ardhini beha, wajma' baynana be-ahsani Ejtimaa' wa aysari E'tilaaf, Fa Innaka Tuhibb-ul-halal wa Takrah-ul-Haram.


Ga addu'ar da larabci:
اللهم ارزقني العلفة وودة و رضاه وارضه بها وجمع بيننا بأحسان اجتماعة ، وايسر اتلاف فإنك تحب الحلال وتكره الحرام

Imam Sadiq (A.S) yace ga wasu ba'adin Sahabban Sa: " Idan Amarya ta shiga ɗakin ku, dukkan ku (Amarya da Ango) ku fiskanci alqibla sai ku fadi wannan addu'ar:
Allahumma be Amanatika akhathtuha wa be kalimatika Estahalaltuha, Fa in Qadhayta Li Minha Waladan, Faj'alhu Mubarakan Taqiyyan min Shi'ati Al-e Muhammad (saww) walaa taj-'al Lish-Shaytani fihi shirkan walaa Nasiba.

Ga Addu'ar da Larabci:
اللهم بأمانتك اخذتها وبكلمتك استحللتها فان قضيتلي منها ولدا فجعله مباركا تقيا من شيهة آل محمد صل الله عليه وآله .
ولا تجعل للشيطان فيه شركا ولا نصيبا.

Idan kuma miji yana son kusantar amarya da soyayya, to da farko ya karanta wannan addu'ar:

"Allahummar-Zuqni Waladan, waj-'alhu Taqeyyan Zakeyyan; Laysa Fi Khalqihi Zeyaadatan wa la Nuqsaan, Waj-'al Aaqibatahu ila al-khayr"

Ga Addu'ar da larabci:
اللهم ارزقني ولدا ، واجعله تقيا زكيا ولا نقصا، واجعل عاقبته ال الخيرا.

Da zarar za'a shiga duniyar Soyayya sai ya zama ɗaya daga ciki yayi Basmala. INSHA Allah

Allah ya bamu zuri'a ta gari, ya kiyaye mu haifar yaran da zasu zame fitina a gare mu.

Daga Wakilan Mu Na Saminaka
Tare da
Bin Haroun Sigau

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post