Da Sunan Allah Mai Rahama Mai Jinƙai.
Tsira da Amincin Allah su tabbata ga fiyayyen halitta Annabi Muhammadu da Iyalansa tsarƙaƙa da Sahabbansa Zaɓaɓɓu.
Assalamu Alaikum wa Rahmatullahi Wa Barakatuhu.
Gabatarwa
Da fatan Allah Ya amsa mana ibadunmu, Ya Gafarta mana, Ya kuma shiryar da mu TafarkinSa Madaidaiciya.
Da farko ina kira ga mai karatu yayi haƙuri ya bi rubutun har zuwa ƙarshe.
Na kasa wannan rubutun ne zuwa kashi-kashi don samun sauƙin karatu.
Idan mai karatu yayi karo da wani abu da ya saɓawa fahimtarsa; to yayi haƙuri har sai ya kai ƙarshen rubutun, mai yiwuwa ya fahimci abin da nake nufi daga ƙarshe. Don rubutun bincike ya gaji hakan.
Azumin Bana 1441,2020.
Azumin bana, ta shekara 1441 Hijira, wanda yayi daidai da 2020 Miladiyya, sanin kowane musamman a Nageriya an samu saɓani sosai, wanda ya haifar da samun bayanai da rubuce- rubuce da saututtuka, har ma da bidiyoyi daga Malamai da ɗalibai daban-daban, waɗanda suka yi bayanansu tare da maida hankali zuwa bayyana ɓangarori daban-daban.
Akwai Ƴan'uwa da dama da muka zanta da su game da wannan lamari na Azumin bana kan ganin Watan ɗaukan Azumi, zuwa ga ganin Watan Sallah Ƙarama. To dana yi musu bayanin abinda Allah ya sanar dani sai suka yi ta ƙarfafani cewa da ni ma inyi rubutu iya gwargwado, ta iya yiwuwa in Allah (swt) Ya so, wasu za su amfana da shi.
Tare da fatan Allah (swt) Ya yi mana Jagoranci na wannan Aniyan da muka yi na wannan taƙaitaccen rubutun.
Wannan rubutun nawa zai maida hankali ne a ɓangarorin dana ga suna da muhimmanci, wanda nake son in ɗan yiwa kaina da Ƴan'uwana Musulmi ƙarin bayani akan su, (Musamman masu bin Mazhabar Ahlul baiti (as), da kuma a keɓe Ƴan'uwana na Harka Islamiyya, Ƙarƙashin Jagorancin Sayyid Ibrahim Zakzaky (H). Duk da cewa ni ba Malami bane, ɗalibi ne mai yi wa Malamai Hidima.
Don haka duk abinda zan rubuta a iya nawa fahimtar ne, in abin da na rubuta yayi dace da abinda Allah Mahalicci yake so, to muna godiya ga Allah, idan kuma abin da na rubuta ya saɓa da abinda Allah yake so (wanda ina neman tsarin Allah kada in rubuta abin da zai saɓa ma abin da yake so), Ya gafarta mini bisa ƙarfin halin da nayi, da na ce zan yi rubutu akan abin da ya shafi AddininSa Mai Tsarki.
An samu saɓanin ganin Wata a wajen ɗaukan lissafin 1 ga Wata, ya yinda wasu Ƴan'uwa Musulmi Ƴan Shi'a Mabiya Sayyid Ibrahim Zakzaky suka ce sun ga Watan Ramadan ta Shekarar 1441 (h) 2020 (m) da Yammacin ranar Laraba 22/04/2020 sai suka tashi da Azumin 1 ga Watan Ramadan a ranar Alhamis 23/04/2020 a lissafinsu, yayin da Sarkin Musulmi, Alhaji Sa'adu Muhammad Abubakar (III) da kuma Ƙasar Sa'udiyya (Hijaz) da sauran Ƙasashe makwabtan Nigeriya, da yawancin ƙasashen Musulmi suka bada sanarwan ganin Watan Ramadana da yammacin ranar Alhamis 23/04/2020 sai suka tashi da Azumin 1 ga Watan Ramadan a ranar Juma'a 24/04/2020 a lissafinsu. A ɓangare na uku, wasu Al'umman Najeriya masu bin lissafin Wata waɗanda ake kiransu da Ƴan sai mun gani da idonmu, ko kuma ana kiransu da Ƴan Gargajiya, da kuma Ƙasar Iran, da Iraki, da sauran Al' ummar Shi'a a Najeriya, da kuma ƙasashen duniya suka bada sanarwar ganin Watan Ramadan da yammacin ranar Juma'a 24/04/2020, sai suka tashi da Azumin 1 ga Watan Ramadan a ranar 25/04/2020 a lissafinsu.
A wajen ɗaukan Azumin bana an samu ɗauka kashi uku, kenan waɗanda suka yi ɗaukan fari sun yi wuni biyu suna Azumi a matsayin su sun ga Wata, yayin da ƴan ɗauka na uku su kuma suka yi kwana biyu suna shan ruwa a matsayin basu ga Wata ba.
A hakan aka tafi har zuwa ƙarshen Watan Ramadana inda aka sami saɓani mai matuƙar yawa da cece-kuce, inda waɗannan adadin Ƴan'uwa Musulmi Ƴan Shi'a Mabiya Sayyid Zakzaky (H) waɗanda suka yi ɗaukan fari rannar Alhamis 23/04/2020, sai suka ce sun ga Watan da yammacin Alhamis 21/05/2020 don haka suka yi Sallah ƙarama ranar Juma'a 22/05/2020, wato sunyi Azumi 29 kenan, Su kuma Sarkin Musulmi da Ƙasar Sa'udiyya (Hijaz) da Iran (wasu) suka bada sanarwar ganin Wata da yammacin ranar Asabar 23/05/2020 suka yi Sallah ƙarama ranar Lahadi 24/05/2020, yayin da sauran wasu Maraji'an Shi'a suka yi Sallah ranar Litinin 25/05/2020.
Anan zamu ga cewa tsakanin Ƴan Shi'a Mabiya Sayyid Zakzaky (H) da suka yi Sallah ranar Juma'a 22/05/2020 sunyi wuni 3 suna shan ruwa a matsayin sun ga Wata. A yayin da Mabiya fatawar Imam Khamene'i (RA) da Sayyid Sistani (H) suka yi wuni 3 suna Azumi a matsayin basu ga Wata ba. Wannan yasa bana akayi kwana huɗu daban-daban ana Sallah, wato an samu saɓanin kwana 4, wanda lallai ba zai yiwu ace duka a kan daidai suke ba, don a Watan Musulunci saɓanin da ya wuce kwana daya to lallai akwai waɗanda suka yi kuskure ballantana kwana uku.
Anan za muyi nazarin yadda al'amarin ya kasance domin tantancewa da dubi sosai, domin muyi gyaran inda muka ga akwai kuskure don kada mu sake maimaitawa, domin kuwa tabbas za a samu waɗanda ko ya zamanto sun ɗauki Azumi cikin Watan Sha'aban suka ajiye cikin Watan Ramadan, wasu kuwa ko sun sha ruwa a farkon Ramadan, ko kuma sun yi Azumi cikin Shawwal.
Amma bari muyi binciken tarihi mai yiwuwa ba zai rasa tasiri da yayi wajen kawo wannan saɓanin ba, da fatan Allah yayi mana Jagoranci.
Za mu ci gaba insha Allah...
28/05/2020
T.A. ATEEQ
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar ilimi
