Abubuwan Dake Jawo Taɓarɓarewar Aure A Ƙasar Hausa



DASUNA ALLAH MAIRAHAMA MAI JINKAI TSIRA DA AMINCIN ALLAH SUTABBATA GA IYALAN GIDANSA TSARKAKA DA SAHABBANSA NAGARGARU BAYAN HAKA ASSALAMU ALAIKUM WARAMTULLAHI (T W) AFARKO ABINDA KE JAWO TABARBAREWAR AURE 1. KARYA

Duk zancen da za a yi wajen neman aure tsakanin namiji da mace, dole ne afaɗi gaskiya namiji yafaɗi gaskiya dangane da matsayinsa ko saminsa, ita ma mace ta faɗi gaskiya dagane da gidansu da matsayin mahaifanta
Ya tabbata a hadithi Manzan Allah (SAWW) yace:
"Ku yi gaskiya, domin gaskiya tana kai mutum zuwa ga nagarta, nagarta tana kai mutum aljanna, mutum ba zai gusheba yana gaskiya face Allah ( SWT) Yasa an rubutashi acikin masu gaskiya.

Ku guji ƙarya, domin ƙarya takan maida mutum fajiri, fajrci kuma yana kai mutum wuta, mutum ba zai gusheba yana ƙarya, har sai an rubutashi awurin Allah amatsayin maƙaryaci''
Amma abin da ke faruwa ayanzu shine, a lokacin da namiji ke neman mace da aure, zaita yimata ƙarya ta hanyar faɗin abin da baikai matsayinsaba, da isar da batakai tasaba. Idan zaizo zance, zaiyi mota da kayan sawa dacin bashin kuɗaɗe, har da sata don yayi mata kyauta da sayen kayayyakin zance dayin kayan lefe. Ita kuma, sai tayi ƙaryar gidan da banasuba don gidansu ƙasƙantaccene, ko tayi ƙaryar iyayan da ba natba, don kasancewar su talakawane.

Sakamakon wanna ƙarya shine, ko da anyi wanna auren ana san juna, daga baya sai mijin yagane cewa ashe ƙarya take, ko matar tagane ƙarya sukayi wa juna. To, anan sai auren ya lalace ta hanyar rabuwa don anƙi fito da wasu bayanai lokacin neman auren, sai da aka tare sananan suka bayyan, ko kuma inba arabuba to daga wannan lokacin ba ƙimanta juna da mutuntawa. Zanmu cigabah insha allah

 KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post