WANDA YA JAGORANCI KAMA SHAIKH ZAKZAKY

Wanda ya jagoranci rundunar sojojin Nigeria wajen cigaba da kai hare-haren ta’addanci akan ‘yan uwa Musulmi a Husainiyyah Bakiyatullah, gidan Shaikh Zakzaky da ke gyallesu da kuma Darur-Rahma, wani Bawahabiyen soja ne mai suna Col. Abdul Khalifa Ibrahim (L).

 Col. Abdul Khalifa, shine Kwamandan Internal Security na 1 Division na Nigerian Army. Kuma shine shugaban rundunar ‘Operation Yaki’ da ke kunshe da wasu sojojin musamman a jihar Kaduna.

 Ya bayyana da bakinsa a gaban kwamitin JCI a yau Laraba 26/4/2016 cewa, lokacin da Burutai ya je Zariya shi ba shi a Zariya din ma kwata-kwata, dan haka GOC ne ya kira shi a waya ya sanar da shi cewa ya shirya sojoji su tafi Zariya saboda ‘yan Shi’a sun tare COAS (Burutai).

 Idan za ku iya tunawa, a ranar Asabar din 12/12/2016 tun da misalign karfe 12:30nr aka zo aka jibge sojoji a gaban gidan Man da ke tsallaken Husainiyyah, wanda tambayar su dalilin zuwa a jibge su a wannan wajen yasa suka yi shirin harbi, sai ‘yan uwa suka fara kabbara, nan take sojojin suka bude ma ‘yan uwa wuta, suka kashe wasu adadi, wanda a nan ne ‘yan uwa suka samu suka iya kora sojojin daga wajen. Sannan suka dauko taya da duwatsu suka saka hanyoyin don kar su sake dawowa.

 Shi kuwa tawagar COAS (Burutai) bata zo wajen Husainiyyah ba sai bawan faruwar wancan abin, suka iso da misalin karfe 2:30nr, wanda wannan ne ya sa ‘yan uwa cikin fushi suka ce lallai ba su aminta da kowane jami’in soja ba, domin ba a jima ba sojojin suka zo suka budewa ‘yan uwa wuta suka kashe ‘yan uwa, suka jikkata wasu da a lokacin suna cikin Husainiyyah wasu ana musu magani.

 Wannan yasa sai suka sake budewa ‘yan uwa wuta suka wuce ta gaban Husainiyyah din. Shi yasa a Video din da sojojin suka dauka suka yada suka yanke yadda aka yi suka wuce din, sai kawai suka nuna gashi ma har sun wuce lafiya ne. nan kuwa bude wuta suka yi suka kashe mutane sannan suka wuce.

 An yi wannan abin ne duka da misalin karfe 3nr, kuma Burutai ya wuce. Amma bayan hakan ne sai GOC ya kira Col. Abdul Khalifa ya bashi umurnin ya zo Zariya, inda shi Abdul din ya bayyana cewa, ya taso ne da rundunar sojoji da misalin karfe 5ny ya iso Zariya da karfe 6ny.

 Col. Abdul ya bayyana cewa, yana isa Zariya sai GOC ya bashi umurnin su je duk guraren da suke mallakin Harkar Musulunci ne su yi bincike, kuma su kamo musu Shaikh Zakzaky, saboda sun samu labarin cewa ‘yan uwan suna ta gayyato mutane za su tada rikici.

 Shi Col. Abdul Khalifa shi ne aka ba wuka da namar cigaba da kashe ‘yan uwa Musulmi tun daga wannan ranar ta Asabar 12/12/2016 da misalin karfe 6ny har zuwa ranar Laraba 16/12/2016. Shine ya rabawa wasu kwamandojin da suke karkashinsa aiki, inda ya tura wani mai suna Col. Babayo da sojoji sama da 40 zuwa Darur-Rahma, ya kuma tura wani Col. Bulaya Husainiyyah, sannan kuma ya tura wani O.O Odufuwa zuwa Gyallesu.

 Idan baku manta ba Col. Babayo shine wanda ya bayyana cewa an tura shi Darur Rahma ne da karfe 5 na Asubahin ranar Lahadi, inda ya riske ‘yan uwa suna Sallah a masallaci, sai yaje don ya yi magana da su, a cewarsa, sai suka yo kansa suka masa dukan tsiya, har suka kwace bindigarsa AK47 wacce ya durawa harsasai 60 suka yi ta kokarin harbawa suka kasa, sojojin da suke karkashinsa su 40 suna tare da shi, amma har wata mace ta zo ta shake wuyarsa ta sumar da shi, daga nan bai farfado ba sai a gadon Asibiti.

 Kunga ya bayyana cewa sun ga ‘yan uwa suna Sallah ne, kuma ba su iya harba bindiga ba, amma sai da suka kashe duk ‘yan uwan da ke wajen nan. Sannan suka rushe gaba daya gine-ginen Darur Rahma wanda suke dayawa kai kace wani kauye ne mai zaman kansa.

 Haka idan ba ku manta ba, Gwamnatin Kaduna ta bayyana cewa ita da Sojoji sun rushe gine-ginen Harkar Musulunci ne, saboda sakamakon musayar wutan da aka yi, gine-ginen sun tsagen da za su iya fadowa akan wani, dan haka suka rushe su. To dan Allah karyarsu ba ta yi karo ba a nan? Wane musayar wuta ne aka yi a Darur Rahma tsakanin sojoji dauke da AK47 da kuma daidaikun ‘yan uwan da soja da kansa ya tabbatar da cewa ba su ma iya harba bindiga ba balle su mallaketa!?

 Gyallesu kuwa, wanda ni ganau ne, ina wajen, Sojojin sun zo ne da misalin karfe 10:30 na dare, kuma suna zuwa suka jefawa wani shagon katako na mai shayi abin fashewa, wuta ya tashi, inda suka rika amfani da hasken wannan wutar da suka saka suna kashe ‘yan uwan da suke zaune a gaban Banaden. Cikin awa 1, zuwa karfe 11:30nd sun harbi sama da mutum 40, wanda a lokacin muka yi sanarwar cewa sun kashe mutum 11 a ciki har da mace guda daya, Shahida Nusaiba A. Abdullahi Sokoto da kuma Malam Hamza Yawuri. Dan Allah aka ake zuwa yin binceken makamai? Ko kuwa haka ake zuwa dama a kama mutumin da ake zargi, kamar yadda Col. Abdul yace an tura su ne su yi bincike kuma su yi kamu?

 Wa kuma ya basu umurnin bude wuta da kashe mata da kananan yara da matasa ‘yan makarantu da dattijai masu fararen gemu a tsawon kwanaki hudu cur!!!?

 Col. Abdul ya tabbatar da cewa sun je Gyallesu ne tun a daren Asabar, amma ba su samu kama Shaikh Zakzaky ba sai a ranar Litini. Wanda kuma yace sun tarar akwai mutane daruruwa a ko’ina a cikin Unguwar. Kuma sun kewaye unguwar ne da suka je a tsawon wadannan kwanaki, suna harbin duk wanda suka samu. Amma sai yace sun kama Shaikh Zakzaky da matarsa da wasu mutum uku ne a gidan. Ina sauran daruruwan mutanen da kuka kewaye suke!!!?

 An tambayi Col. Abdul Khalifa a matsayinsa na wanda ya jagoranci dukkan ta’addancin da sojojin suka yi a Zariya, an tambaye shi mutum nawa suka iya kamawa kuma mutum nawa suka iya kashewa, amma yace duk bai san adadinsu ba. wannan kuwa yana tabbatar mana da cewa adadin da suka kashe din sun yawaita ne da sun kasa iya adadinmu ma, na tabbata da sun san adadin da suka kashe basu wuce mutum 100 ba za su ce mutum kusan 100 ne.

 Kuma yace sadda suka bar gidan Shaikh Zakzaky a ranar 17 ga Disamba, sun bar gidan lafiyansa kalau ba tare da an rushe shi ba. Karyar da bata da wajen zama. Mutanen da tun a ranar Lahadi suka kona gidan Shaikh Zakzaky kurmus, suka farfasa shi da gurneti, sannan suka fara baje shi. Amma kunji da ke ba su kunyar karya abin da yake fadi.

 Col. Abdul ya bayyana cewa ya tura sojoji 60 -  60 ne a Husainiyyah da Gyallesu, Darur Rahma kuma sojoji 40 alhali sojojin da suke Husainiyyah tun a ranar Asabar da rana sun haura guda 200. Sannan kuma a wayewar garin Lahadi sun ta karo sojoji daga barikokinsu wanda zuwansu ne suka wa Gyallesu kawanya, bayan sun rushe Gaban Husainiyyah da Ababen fashewa sun Shiga sun kashe na kashewa a ciki.

Wai shin tsoron me sojojin Nigeria suke ji da kowa ke kokarin zamewa akan Ta'addancin Da suka yi? Domin hatta shi Col. Abdul din da yace shi ne jagoran dukkan bangarori sojojin da aka tura su ko ina a Zariya, an tambaye shi wa ya bada izinin harbi yace ba shi bane kuma bai sani ba.

Wani abin raunin hankali kuma a makon da ya gaba ne Col. Babayo ya bayyana cewa shine aka tura Darur Rahma, kuma aka sumar da shi a can bai farfado ba sai a Asibiti, kuma yace har yanzu yana Asibiti ne, daga Asibitin ya zo gaban Kwamitin JCI, amma yau an nemi yana ina Lauyan Soji yace Wai an tura shi wani cos a Kasar waje shi da Col. 0dufuwa wanda shine aka ce ya jagoranci kama Shaikh Zakzaky da kisan kiyashin Gyallesu.

Al'umma na lura da mutanen nan kuwa? Mutanen nan suna sane da cewa suna bayyana wa Duniya su Wawaye ne, Dolaye, sakarkaru, Jahilai, Makaryata kuma matsorata!?

Col. Abdul Khalifa Ibrahim ka tanaji makomarka a wutar Allah (T) bayan kaskancin Duniya da zaka fuskanta. Allah ya bayyana Mana cewa, duk wanda ya kashe Mumini da gangan, sakamakon sa jahannama ne zai dauwama a cikinta, kuma Allah zai yi fushi da shi kuma ya tanada masa azaba mai radadi.

#FreeShaikhZakzaky
#GodProtectZakzaky
#WeAreWithZakzaky

— Saifullahi M Kabir
26/4/2016 — 19/7/1437

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post