"Shi Musulunci yana kallon insaniyya ne (Humanity) wato 'yan adamtaka, shi yasa mu bamu gaba da kowwa ko da bashi da addini, domin zamowwar sa Mutum ma kawai ya wadatar mu yi abota da shi.
Amma idan ana maganar Fahimtar addinin shiriya ne (Musulunci) to ba bukatar sai ka ce wa kirista ko wanda ba musulmi ba, dole sai yazo yayi addininka na Musulunci ba, kai ba bukatar ma kace masa ya shiga Musulunci.
Almuhimmu shi ne ka kira shi da dabi'un ka kyawawa, tare da nuna karamci da gaskiya cikin magana da aikin ka. Idan Allah ya nufe shi da shiriya to ta haka zai ji shawa'ar addinin ka.
Shi yasa mu muka ce ma, da za a samu wani rikici (ba fata muke ba) to zamu ba duk wanda ba Musulmi ba kariya, yazo muhallin mu ya zauna har ma idan lokacin Service (Church) din sa yayi zamu bashi wuri yayi abinsa, idan na rana yake zamu yi sallah, idan mun gama mu tashi yazo yayi service dinsa na rana, haka na dare, haka ma na safe. Kuma zamu ciyar dashi... Sannan ba zamu taba ce masa ko "ko zaka musulunta?" har lokacin da zai tafi abinsa, Allah basshi shi da kansa zai yi tunani tunda Allah ya bashi hankali da nazari.
Mu haka muka ga Annabi (S) ya zauna da su..."
Shaikh Yaqub Yahya Katsina a wani jawabinsa sati biyu da suka gabata.
BARKANMU DA JUMA'A
_Bin Yaqoub Katsina
BinKatsina@gmail.com
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Tunatarwa
