Da'awar Malam Zakzaky (H) Ba Da'awa Bace Ta Aqidah,
Da'awar Malam Zakzaky (H) Wani Yunkurine na Sauke Haqqin Allah (T) Ta Hanyar Biyayya ga Umarninsa da Hanuwa ga Hane-hanensa da Kuma Qoqarin Kawo Gyara Acikin Al'umma don a Gudu Tare a Tsira tare agobe Qiyama.
Al'umma Tayi Nisa cikin Dimuwa da rashin sanin hakkokin Allah a kanta an ajiye umarnin Allah (T) a gefe anata rayuwa cikin Son Zuciya da makanta wannan ya jaza Dinbin matsaloli a Tafarkin rayuwar Al'umma kama daga Munanan Dabi'u, da Hakaye, Keta, da Fin karfi,Zalunci da Danniya, Jahilci da makanta, Rashin sanin Addini da Rashin sanin Alkibla, da kuma uwa uba fuskantar mummunar makoma a gobe kiyama.
Wannan yasa malam Zakzaky (H) ya tashi domin kiran mutane zuwa ga Addini Wanda a cikinsa ne Kawai Mafitarsu take.
Sa6anin Yadda Al'umna Suka Jahilci Kiran NASA Da Yawan Al'umma Sun Dauka Cewa Malam Zakzaky Yana Kirane Domun Jama'a Su Bishi Ya Zamto Yana Mulkarsu.
Tags:
Jagoran Gaskiya
