Yin Tafiya Da Annanbi (S.A.W.W), Bai Kai Kwanciya Kan Gadon Sa Ba!!





@ MA'ASUMAH NIGERAN NEWS UPDATED @

GASKIYAR DA WASU BA SA SON JINTA KENAN

Wani lokaci mutum kan kauda kai, amma sau da yawa maganganun wasu kan sa dole ka numfasa don ka bayyanar da gaskiya masu rabo su rabauta .

Za ka ji wasu na cewa wai Abubakar ne Khalifan farko bayan Annabi (S.A.W.W ), amma cikin maganar tasu babu nassi sai dai ka ji ana ba ka wasu misalai wadanda hankali ma ba zai dauka ba ballantana sharia .

Daga cikin hujjojin sukan ce wai Abubakar ne ke jan sallah a halin rashin lafiyar Annabi (S.A.W.W ), kuma wai shine abokinsa a halin hijra .

Babu musu kan batun tafiyarsu tare a halin hijra zuwa Madinah , sai dai darajar zabarsa a matsayin abokin tafiya bai kai darajar wanda aka kira don ya kwanta kan gadon fiyayyen hallita (S.A.W.W )ba .

Dalili kuwa shine, shi wanda aka zaba ya zama abokin tafiya bai samu kalmar yabo daga wani ba, sai dai ma mu fassara da cewa zarginsa akayi.

Allah (T )na cewa,

‘’ IDAN BA KU TAIMAKE SHI BA ALLAH YA TAIMAKE SHI YAYIN DA KAFIRAI SUKA FITAR DA SHI YANA NA 'DAYAN BIYU, YAYIM DA SUKE KOGO , YAYIN DA YAKE CEWA ABOKINSA ,‘’ KADA KAYI BAQIN CIKI, LALLE ALLAH NA TARE DA MU ....‘’

     (TAUBA:40)

Kunga anan idan ba ka kira shi da cewa zarginsa aka yi ba ba za kace an yabe shi ba.

Shi kuma wanda ya kwanta kan gadon Manzon Allah yabo ya samu daga Allah (T ).

‘’ DAGA CIKIN MUTANE AKWAI WANDA YA SAYAR DA RANSA DON NEMAN YARDAR ALLAH , KUMA ALLAH MAI TAUSAYI NE GAME DA BAYI .‘’

  (BAQARA:207)

Kunga anan indai batun fifiko ne ba za a hada wanda aka zarga da wanda aka yabe shi ba.

‘’ BA ZA TABA ZAMA DAIDAI WAJEN ALLAH BA. ‘’

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

       09039791509

~17th May, 2020.

KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post