Mutane Kashi Uku (3) Ne – Inji Imam Ali (AS). Fita Na Ɗaya (1)





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KAI KUWA CIKIN WANNE AJI KAKE?

Wata rana Imam Ali (A.S )ya yiwa Khumail Bn Ziyad bayani kan matsayin ilimi , inda Khumail yake bayyanawa cewa;

Wata rana Ali (R.A )ya kama hannuna muka tafi wata maqabarta, yayin da muka bulla sahara sai ta ja numfashi sannan yace;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Yaa Khumail , su fa wadannan zukata guraren ajiya ne, amma mafi daraja a cikinsu ita ce wacce tafi kiyaye magana, dan haka ka kula da abinda zan gaya maka.

Su dai mutane kashi uku ne:

(1)- Akwai malami mai bin Allah .

(2)- Akwai dalibi mai neman sani dan ya sami tsira .

(3)- Saura kuma ganyar sodi ne ('yan abi yarima asha kida), duk wanda yayi kira za su bi shi (duu kamar an tsayar da Buhari takara kafin ya hau karagar mulkin siyasa ), duk inda iska ta kada sai su bi, ba sa neman su haskaka da hasken ilimi , kuma ba su jingina da wani babban bango ba .

Yaa kai Khumail , ka sani cewa shi ilimi shine gaba da dukiya , dan kuwa ilimi shi ke ba ka kariya , amma ita dukiya kai ke kare ta, ciyar da dukiya na rage ta (a zahiri ), amma ciyar da ilimi na qara shi (zaahiran wa baadinan ), sannan duk abinda dukiyar tayi yakan gushe in babu ita.

Yaa Khumail , shi fa ilimi rance ne ake bada shi, da shi mutum kan bi Allah (S.W.T )a rayuwarsa, zai kuma sami kyakkyawan sakamako bayan mutuwarsa. Shi ilimi jagora ne, ita ko dukiya jagorantarta ake yi ...‘’

ZA MU CIGABA INSHA ALLAH.

Tare da Ado Isah Guda .

       09039791509

~16th May, 2020.

  KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post