@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KAI KUWA CIKIN WANNE AJI KAKE?
CIGABA:-
‘’ Yaa Khumail, masu tara dukiya jahilai matattu ne ko da kuwa a raye suke, amma malamai (na kirki )har abada suna nan ko da sun mutu , idanu ba sa ganinsu , amma aikinsu nanan cikin zukatan jama'a.‘’
Khumai yace ;sannan yayi nuni da yatsansa zuwa qirjinsa yace;
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ Haqiqa nan akwai tarin ilimi mai dimbin yawa, ina ma na sami masu daukar ilimin, sai dai wadanda na samu ba amintattu bane, suna amfani da harkar addini domin samun duniya, suna tinqaho da ni'imomin Allah bisa bayinsa da wakilansa, da kuma waliyansa . Ko suyi jayayya da masu bin gaskiya marasa basira . Gane hanyarta (ita gaskiya ), sai shakka ta shiga zuciyarsa nan da nan saboda wauta ya rude , sai yayi amfani da ilimi ya zama mahandami, mai jin dadi mai miqa wuya ga son zuciya, ko kuma hadamamme mai tara dukiya mai boye ta (ga mabuqata ).
Irin wadannan mutane ba su dace su zamana jagororin addini ba, abinda suka fi kama da shi shine dabbobi masu cin ciyawa. To, da hakane ilimi yake mutuwa idan masu dauke da shi sun mutu .‘’
(NAHJUL-BALAGHA (ta'aliq ), shafi na 633. (Bugun Mu'assatu Darul Hijra ))
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~17th May, 2020.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Taskar ilimi
