Ya kamata a janye mana dokar lock down



                              lock down


da akwai cutar Corona-virus, amma dai a nan Nijeriya ni ban yarda da irin kididdigar da hukumomi da gwamnatoci suke bayarwa. Gwamnatinmu gwamnati ce wacce ta kware wajen karya da yaudara, to ta yaya zan yarda da abinda ta ke fada? Wallahi ni ko menene gwamnatin Nijeriya ta fada bana yarda, sai dai idan na ga zahiri ko na samu tabbaci daga wanda na ke da yakinin bazai yi karyar ba.
Yanzu lissafin da NCDC ke bayarwa shine wai wadanda suka kamu da Corona-virus a Nijeriya sun kusan dubu biyu, amma duk wadannan mutanen babu wanda ya taba ganinsu, babu wanda ya taba ganin hoto ko bidiyon masu Corona-virus a Nijeriya, idan da gaske ne sai a dauki 'yan jaridu su je su gano su zo su sanarda mu. Suma 'yan jaridun sai su sanya kayan kariya suje su gano mana inda ake killace da masu cutar, duk duniya haka ake yi, amma mu nan da yake babu gaskiya anki a nuno mana masu cutar, su kansu 'isolation centers' sai a nuna mana ko hotuna ne muga kudadenmu din da ake cewa an kashe.
Don haka wannan siyasar da suke yi da Corona-virus ya kamata su dena, mu kawai a bude mana kasuwanni mu cigaba da harkokinmu, babu wani "stay at home". Hatta a China inda cutar ta fara bulla an ce yanzu babu mai ita, har ma sun fara bude Makarantu da Ma'aikatu. Ko'ina a duniya lissafi na nuna cutar nan baya take yi, amma mu kullum sai ace mana wai abin karuwa yake yi.
Dukkanin matakan kariya don gujewa yaduwar wannan cutar a Nijeriya aikin banza ne, Nijeriya kasa ce wacce zaman gidan nan bazai taba yiwuwa ba, a unguwanninmu na talakawa ko ruwan wanke hannu babu, balle wani 'sanitizer'. gwamnati ta riga ta baro shiri tun rani, bazai yiwu ba dokar da aka sanya a Amurka, Faransa, Ingila China, Iran da Jamus ka zo ka ce wai muma zaka sanya mana ita, ko ba komai a chan kasashen an wadata al'umma, babu wani wanda ke kwana da yunwa, kuma ko a 'Lockdown' din gwamnatoci na taimakawa da mutane da abinda zasu ci. Kuma mu ma nan bawai gwamnati baza ta iya taimakawa mutane da abinda za su ci ba ne, a'a kawai tsabagen mugunta da keta ce ta masu mulkinmu. Yau da ace irin kudade da abinda ake cewa an warewa talakawa don saukaka masu zaman gida yana kaiwa hannun talakawan da babu wanda zai yi korafi, kawai mu an fake da Corona-virus ne ana satar kudaden talakawa. An ki a baka abinci kuma ace baza ka fita ka nema ba, wannan ai zalunci ne!
Ai gwamnati ta san yadda zata magance cutar nan ba sai an yi "stay at home", ba. Tun farko ma ai laifin gwamnati ne, bata tashi rufe shigowa kasarnan ba sai da kowa da kowa ya dawo daga kasashen waje. Sannan ta zo tana wani burgar banza wai an hana shigowa daga Amurka, China, Iran da sauransu. alhalin riga an shigo da 'virus' din. Kuma ko daga baya kamata yayi a sanya doka mai tsanani, kar wani ya shiga wata jahar, kuma a kiyaye duk matsayin mutum kar a barshi, (amma a cikin jahohi a kyale mutane su nemi kudi da abinci). Duk ba a yi ba sai yanzu za a zo ana ta faman takura mana wai ana yakar Corona-virus, mu talakawa abinda ke damun mu shine 'Hunger-virus' (wato cutar yunwa). ita ce kullum ta ke kashe talakawa, ita ce kullum ta kewa talakawa illa. Al'umma basu da matsala don an rufe Masallatai da Chochina, da farko kawai a a bude mana kasuwannci mu nemi kudade da abinci.
Banda tsabagen rashin tausayi 'yan shinkafa gwangwani biyun da aka rabawa wasu talakawan ita ake nufin zasu ta ci har bayan sati biyu, ballantana mu da aka ce wai sai nan da kwana talatin zamu fita, ranar Larabar idan ka dan fita ina ka nemi kudi balle ma ka sayi abinda zaka ci? Ace wai a sati daya sau daya zamu fita, fitarma sai sayo abinci, ina kudin suke balle ma a sayi abincin? Irin wannan ai gwara mutum ya zo da bindigu duk ya kashe mu. Don duk wanda ya sanya mana dokar nan so yake ya kashe mu da yunwa.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post