Wafatin Nana Khadijah (S.A), 10 Ga Ramadhan!!





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

KIN KYAUTATA, KUMA ALLAH YA KYAUTATA MIKI

Sayyidah Khadijah (S.A)ita ce mace ta farko wajen Manzon Allah (S.A.W.W), wacce tayi imani da shi tun farkon wahayi, ta zauna tare da shi hai ta haifa masa 'ya'ya abin alfahari wadanda suka zama abin riqo kuma ma'auni da ake amfani da shi wajen gane muminai.

Ta bawa Annabi (S.A.W.W)kariya da kuma taimakonsa da dukiyarta wajen isar da saqon muslimci. Babu wata mata wacce tarihin muslimci ya kawo gudumawarta a addini kamar ta. Sannan ita ce kadai wacce ta sami yabo daga Allah tun a duniya.

Ta kyautata zamantakewar aure ga mijinta wanda ta zama samfuri abin koyi ga dukkan mata muminai.

Da ace mata na koyi da ita a aikace, lalle da mazajensu ba za su taba yi musu kishiya ba, Sayyidah Fatimah (S.A)ta zama babban abin misali domin ita ma mijinta bai yi mata kishiya ba har ta rasu.

Anyi mata bushara da gidan Aljannah tun tana dumiya.

Manzon Allah (S.A.W.W)na cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ LALLE ALLAH YA UMARCE NI DANA YIWA KHADIJAH,BUSHARA DAWA NI GIDA A ALJANNAH DAGA BENAYE, BABU WANI QUNCI KO WAJALA A CIKINSA .‘’

-Bukhari, J:3, SH:70

-Muslim, J:7, SH:133.

Saboda tsananin son da Annabi (S.A.W.W)ke yi mata, ya riqa yawaita ambaton sunanta bayan wafatinta, tare da kyautatawa qawayenta.

Ta rasu ne ranar 10 ga Ramadan, shekara goma (10)bayan manzanci, wato shekara uku kenan kafin Hijrah.

AMINCI YA TABBATA A GARE KI A RANAR DA AKA HAIFE KI DA RANAR DA KI KAYI WAFATI, DA KUMA YARAR DA AKE TASHINKI KINA RAYAYYIYA

Daga wakilanmu na Bauchi zone.

Tare da Ado Isah Guda.

        09039791509

~2nd May, 2020.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post