Wata Daban| Mace-Mace Na Qara Zama Barazana A Najeriya




---Albarno. Mahdee A Imam

Yawan mace - macen dake faruwa a kasar mu ta Nigeria musamman arewacin Nigeria yana dada tada hankalin mutanen yankin .

Wannan mace macen ba karamun tada hankula yake ba .

Ita de wannan mutuwa ta saba ma hankali ta banbanta da irin mutuwar da mutanen Alummar yankin suka saba gani .

A binciken da mukayi mun gano akalla garuruwa Hudu a arewacin Nigeria da mace macen yafi yawa .

jihohin sun hada da sokoto , kano , katsina , Jigawa da kuma borno .

Mun fara da jihar jigawa karamar hukumar hadejia inda a cikin kwanaki basu wuce 10 ba mutum 100 suka mutu .

Inda yanzu gwamnatin jihar jigawa ta kafa kwamitin bincike akan yawan mace macen da kuma musabbabin mutuwar .

 A jihar jigawan an nada kwamishinan lafiya dr zakari akan shugaban kwamitin inda ake sa ran ze mika rahoton nan da kwanaki uku .

Sannan a cigaba da bincike munje jihar sokoto shima inda mace macen ya taazara alummar garin .

Gwamnan jihar yakafa kwamitin bincike da kuma bude kundin rigista a makarbartun jihar domin sanin adadin mutanen da ake binnewa a kowacce makabarta a rana .


Su jihar sokoto ma gomman mutane ke mutuwa a ko wacce rana wannan shine yakara tada hankalin masu gine ginen kabarburan na garin .


Sannan a jihar ta sokoto an samu bullar cutar ta corona inda mutane 66 suka kamu mutum 8 suka mutu har yanxu su baa samu wanda ya warke ba a jihar .


A jihar maiduguri ma baa barta a baya ba gurin yawan mace macen inda su kuma manyan jihar da talakawa ke ta mutuwa .

Inda a cikin kwanakin sunce kullum se an kai gawa makarbata wato kullum se an mutu .

Inda a Unguwar quaters na makarantar government college mutane 6 suka mutu a lokaci guda .

Se jihar katsina inda alummar yankin su ma suka shaida mana cewa mace macen da ake yi musu basu taba ganin irin shi ba yatada masu da hankula ba kadan ba.

Su kuma kano abun yafi na ko ina tsanani inda da ake tunanin yunwa ke kashe su .


Se gashi harda manyan jihar , da ya hada da malaman jamia , sarakunan jihar ,da shuwagabannin yan sanda , har da likitocin jihar ,da kuma yan kasuwa , da kuma talakawan , garin inda mutanen jihar a cikin kwana biyu sama da mutum 200 suka mutu .

Abun da yafi tada hankalin su shine mutuwar sama mutum 50 a unguwa daya kawai kuma inda yawancin wanda suka rasun maza ne
Kuma ba wani ciwo bane illa zazzabin kwana biyu batare da doguwar jinya ba .

Wasu mazauna garin sunce harda zaman gida da akeyi da kuma yunwa da ake fama da ita a jihar .

An bizne gawarwakin ne a makabartu guda uku na jihar banda wanda ake rufewa dayawa a lokaci guda a cikin kananan hukumomin dake a garin kano din

Sannan matsalar corona na ta karuwa a jihar inda yanzu harda likitocin jihar ke fama da corona inda adadin wanda suka kamu yafi ko ina yawa a arewacin kasar. KU KARANTA 

WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post