Daga Yahaya Muhammad Soje
A yanayin da ake ciki na mummunan cutar korona bairos da kuma zagayowar ranar tunawa da aikin Jarida na Duniya, Jami'an tsaron Nijeriya sun sake murkushe hakkin Yan Jarida wajen hanasu saka Tafsir din Jagoran Harkar Musulunci mabiya mazhabin Shi'a Shaikh Ibraheem Zakzaky
Jami'an tsaron DSS sunyi ma babban gidan Rediyon na Jihar Nasarawa wato NBS Keffi Dirar mikiya tare da yi musu barazana kana kuma suka dakatar da saka Tafsirin Jagoran Mabiya Mazhabin Shi'ar Shaikh Zakzaky suka kuma Kwace Memory din Tafsirin Malamin.
Gidan Rediyon NBS Keffi Wanda suka dauki tsawon shekaru masu yawa suna saka Tafsirin Malamin, sai dai wannan karon Jami'an tsaron sun hana ba tare da wata Hujja ba.
Kwanaki biyu da suka gabata ne dai masu bibiyar wannan gidan Rediyon na NBS Keffi suka ji shiru akan Jawabin Malamin.
Ko menene dalilin hukumar DSS na aikata wannan mummunan aikin?
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Labaran Duniya