Wanda Bai Damu Da Al'amarin Musulmi Ba Baya Daga Cikin Su.!!

De




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

MATSALAR PALESTINE MATSALARMU CE

Ko ba komai ita zuciya Allah ya dora mata son mai sonta da kuma qin maqiyinta, ba zai taba yiwuwa ka sami son wadannan abubuwa biyu cikin zuciyar mutum baba.

Babu wani batun cewa wannan mutumin musulmi ne ko ba musulmi, duk yadda ya kasance shine fassarar matsayinsa a wajenka. Za ka iya samun mutum musulmi amma tsananin qiyayyar da yake nuna maka ta kai yadda ba ya son rayuwarka ko wani abu na cigaban rayuwarka.

Amma abin mamaki kuma sai ka tarar wanda ba musulmi ba na tausaya maka tare da fatan wanzuwar rayuwarka.

Babban abinda nake son jawo hankalinmu anan shine batun halin da 'yan'uwanmu musulman PALESTINE ke ciki na takurawa da gallazawa daga hannun Yahuwa wanda hakan takai suka karkashe su bayan hanasu yin ibada a dakin Allah (MASALLACIN QUDUS).

Motsawarka ta kowacce fuska na taimakawa tare da farranta zuciyar wanda ka nuna kana tare shi, kuma yakan qara masa qwarin gwiwa kan jajircewar da yake yi kan wannan abinda yake yi.

Ba ma harkar addini ba, ko da ace aikin banza mutum ke yi sai kuma yaga jama'a na goya masa baya, to, zai dage sosai kan wannan abinda yadoru a kansa.

Saboda haka al'amarin PALESTINAWA na dukkan musulmi ne ba wai na qabilanci ko qungiyanci ba, idan na fadada kuma sai nace al'amari na dukkan masu tausayi da qyamar zalunci, domin naga har wadanda ma ba musulmi suna fitowa wannan nuna qyamar abinda Yahudawa ke yi na keta alfarmar 'yan adamtaka kan raunanan PALESTINAWA.

Manzon Allah (S.A.W.W)na cewa;

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ DUK WANDA BAI DAMU DA AL'AMRIN MUSULMI BA, TO, BA YA TARE DA SU .‘’

😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭

FREE PALESTINE !

     Ado Isah Guda

~15th May, 2020.
KU KARANTA 

WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post