Masallacin Qudus ( Baitul-Mukaddas) shine al-Kiblar farko ga al'ummar Musulmi, kuma Masallaci na uku (3) mafi daraja bayan Masallacin Ka'abah da Masallacin Annabi Muhammad(S) da ke garin Madinah. Shi kuma Palasdinu Wuri ne da aka saukarwa Annabawa(AS) wahayi. Sannan kuma Palasdinu wani yanki ne na tarihin Musulmi, doriya akan kasancewarsa Masallacin Qudus alkiblar musulmi ta farko kuma gurin da Annabi Muhammad(S) yayi Isra'i kafin Mi'iraji, yayinda Annabi(S) ya jagoranci Annabawa(AS) sallah a masallacin Qudus.
Ranar Jumu'ar karshen ko wane watan Ramadan, rana ce da Ayatullah Imam Khomeini(QS) ya ayyana a matsayin Ranar Qudus ta duniya. Ma'ana ranar da za a fito domin nuna ma duniya cewa wannam masallacin namu ne (Musulmi), kuma a nuna rashin amincewar mu da zaluncin da Yahudawa ke yi akan musulmin kasar Palestine. Ya ayyana wannan ranar ne tun a shekara ta 1979 (shekarar farko bayan cin nasarar juyin- juya hali na musulunci a kasar Iran).
- Ibrahim Almustapha Saminaka
- 23/Ramadan/1441 KU KARANTA
WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
