WACCE AL'UMMA CE MAFI ALKHAIRI CIKIN AL'UMAR ANNABI (S.A.W.W )???
@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
AIKIN MUTUM KAWAI KE NUNA MATSAYINSA WAJEN ALLAH
Rayuwa tare da Annabi (S.A.W.W )ba za ta taba amfanar da mutum ba har sai yayi imani da shi kuma aikata abinda ya umarce shi ko ya hanu daga haninsa. Wanda ya rayu da Annabi (S.A.W .W )kuma ya kyautata aikinsa, to, ba zai taba zama daidai da wanda ya kyautata aiyukansa a wannan zamani ba .
Haka zalika , dadewarka qarqashin mujaddadi ba zai fifitaka kan wanda ya amsa kiransa a qarshen da'awarsa ba, sai dai kawai in ka fi shi kyautata aiyukanka .
Wasu hadisai guda biyu za su iya zama mana ma'auni na sanin cewa fifiko na samuwa ne kawai ta hanyar aiki .
Ya zo cikin Bukhari daga Annabi (S.A.W.W )na cewa:
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ MAFI ALKHAIRIN QARNONI SHINE QARNINA, SA'AN NAN WADANDA SUKA BISU, SA'AN NAN WADANDA SUKA BIYU SU .‘’
(Bukhari, J:5, SH:2)
A dunqule wannan hadisi na nuna mana ne tamkar na wancan zamanin (SAHABBAI )sun fi a wannan zamani da muke ciki .
Sai dai kuma ya zo cikin Musnad na Ahmad, daga Ammar Bn Yasir, daga Annabi (S.A.W.W )cewa:
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ MISALIN AL'UMMATA TAMKAR MISALIN RUWAN SAMA NE, BA A SAN NA FARKONSA NE KO NA QARSHENSA WANDA YAFI ALKHAIRI BA .‘’
(Musnad Ahmad, J:4, SH:319)
Wannan hadisi kuma yana nuna mana ne cewa gwargwadon yadda albarkar abin yazo shine mafi alkhairi , domin wani lokaci samun ruwan farko shi ke samar da mafi alkhairin amfanin gona, wani lokaci kuma in ba a sami ruwan qarshe mai albarka ba sai ayi hasarar dukkan abinda aka suka.
KYAKKYAWAN AIKINKA SHINE FIFIKONKA WAJEN ALLAH .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~19th May, 2020.
