Tambaya: Menene Sayyadi Ali (A.S) Yayi Wa Wannan Al'umma???



Bismillahi Wassalatu Wassalamu Ala Raaulillahi Wa'alihi Addayibina Addahirina. Yauce Ranar Da Al'imamul Karrar alaihissalam Yayi Shahada. Akan Haka Naga Kyaun Maimata Wannan. Rubutun Domin Sanin Irin Baqin Zaluncin Da akawa Wannan Bawan Allah Da Babu Wani Mutun Cikin Halittu Da Yake Da Martabobi Da Maqamai Da Shi Kadaine Yake Dasu Cikin Wannan Al'ummar. Shine Sirikin Annabi, Dan Uwan Annabi, Sarkin Yakin Annabi, Mijin Shugabar Matar Duniya, Baban Shugaban Matasan Aljanna Sannan Shugaban Kowane Mumini Bayan Annabi Muhammadu S,a,w,w.

Amma Duk da Wannan An Zalunce Shi Da Diyansa Zaluncin Da Tarihi Bai Rubuta Wani Mutun Da Akawa Irinsa Ba Cikin Wannan Al'ummar !!

Sanin Kowane Musulmi Ne Cewa Babban Matsalar Da Ta Raba Kan Musulmi Gida Biyu Sunnah Da Shi'a Itace Matsalar Sahabbai Radiyallahu Anhum.
Sai Dai Abin Baqin Cikin, An Siyasan Tar Da Wannan Matsalar. Kuma Siyasar Sarakuna Ce Ta Assasa Wutar Wannan Qiyayyar, Saboda Akwai Manyan Sahabbai Kuma Ahlin Gidan Manzon Allah Da Aka Kashe Su, Aka Zage Su, Amma Kuma Wadanda Suka Cimu Mutunci Suka Ci Bilis.

HALATTA KISAN IMAMU ALI DA ALHUSSEIN.

Ibnu Hazmin Cikin Littafensa " Almuhalli " 1 / 484.

Hafeez Turkumaaniy Cikin Littafensa " Jawahirul Naqiy Bi Zaili Sunanil Baihaqy " 8/ 58.

lafazin Ibnu Hazmin Ne

لا خلاف بين بين احد من الأمة فى أن عبد الرحمان بن ملجم لم يقتل عليا الا متأولا مجتهد مقدر أنه على صواب "

Babu Sabani Tsakanin Wani Mutun Cikin Wannan Al'ummar Cewa Abdulrahman Dan Muljamin Bai Kashe Ali Ba Face Bisa Tawili Bisa Ijtihadi, Yana Mai Qaddara Cewa Yana Akan Dai Dai.

Wannan Shine Abinda Suka Fada Akan Wannan Zindiqin Da Ya Kashe Imamu Ali.

IMRANA DAN HIDDANA :- Shine Mutumen Da Ke Waqa Yana Kiran Imamu Aliy Da " Sharrul Halqi " Mafi Sharrin Halittar Allah, Haka Yake Kiran Sayyidina Aliy, Amma GA Abinda Malamai Sukace Akansa Bayan Sun Fadi Wannan Ta'asar Tasa.

Alhafeez Zahabiy Cikin Littafensa " Mizanul I'itidal " 5/285 Lamba ta 6383 Yace :-

إن عمران صدوق في نفسه روى عنه فلان وفلان

Shidae Imrana Mai Gaskiya Ne A Kankin Kansa, Wane Dayan Wane Sun Ruwaito Garesa.

Sai Ibnu Hajar Yace Cikin " Tahzibub Tahzib " 8/127

وقال العجلي بصري تابعي ثقة

Ijliy Yace Imrana Dan Hiddana Mutamen Busra Ne Tabi'ine Amitatce "

Abin Tambaya Anan, Ta Yaya Zaka Kira Mutunen Da, Ya Qaryata Annabi Saw Mai Gaskiya ?

Wanda Ya Kira Sayyidiy Ali Da Mafi Sharrin Halittar Allah Amintattce ?

UMARU DAN SA'ADU :- Wannan Shine Tsinanne Da A kasa Yakashe Shugaban Matasan Aljanna Al'imamu Hussein A, s, Saboda Mulkin Duniya.

Ga Abinda Sukace Akansa

Ibnu Hajar Cikin " Tahzibub Tahzib " 7/

كان يروي عن أبيه أحاديث وروي الناس عنه وهو تابعي ثقة، وهو الذي قتل الحسين "

Ya Kasance Yana Ruwaitowa Daga Babansa. Mutane Sun Ruwaito Daga Gareshi, Tabi'ine Amintattce, Shine Ya Kashe Hussein.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'una !!
Wanda Ya Kashe Hussein Amintattce Ne !!

AMINTA MASU ZAGIN IMAMU ALI MAFI SHARRIN ZAGI.

Malamman Jarhi Da Ta'adeel Sun Wassaqa Mutane Zindiqai Fasiqqai Saboda Siyasar Sarakuna.

GA Misali

Khaleed Dan Abdullahi Alqisariy :-

Zahabiy Yace cikin " Siyaru "

وكان ممدوحا جوادا معظما عالى الرتبة من نبلاء الرجال وفيه نصب "
Ya Kasance Abin Yabo, Mai Baiwa Ne, Wanda Ake Girmamawa, Mai Madaukakiyar Marbata, Yana Daga Cikin Manyan Mazaje, Sai Dai Akwai Nasbi Tattare Dashi ( Maqiyin Ahlul Baeyt)

yaci gaba da cewa :-

قال فضيل بن زبير سمعت القسري يقول فى علي ما لا يحل ذكره "
Fudail Yace Naji Qisariy Yana Fadar Wata Magana Akan Ali Dai Bai Halatta A Fadeta Ba.

Wannan Maganar Daya ke Fada Itace, Gata Cikin " Ansabul Ashraf 9/59 Aghaniy 2/28 👇👇

لما كان أمير العراق كان يلعن عليا فيقول :- اللهم العن عليا بن ابي طالب بن عبد المطلب بن هاشم صهر رسول الله على ابنته، وأبا الحسن والحسين " ثم يقبل على الناس فيقول :- هل كنيت ؟

lokacin Da Ya kasance Sarkin Iraq Ya Kasance Yana LA'antar Sayyidina Ali, Sai Yace Akan Minbari " Ya Allah Ka LA'anci Ali Dan Abu Dalib Dan Abdulmuddalib Dan Hasheem, Surukin Manzon Allah Akan Yarsa, Baban Hassan Do Hussein. Sannan Ya Juyo Ya Fuskancin Mutane Yace :- Shin Nayi Kinaya ?

Amma Duk Da Haka, Zahabiy Yace Mai Gaskya Ne. Ibnu Hibban Yace Amintattce Ce.
Bukhari Ya Karbi Hadisinsa Da Abu Dawud.

ka duba " Siyaru da Tahzibub Tahzib "

HURAIZU DAN USMAN

ka Duba " Tahzibub Tahzib " 2/239 Da Muqadimatul Fathul Baariy " Na Ibnu Hajar Yace :-

قال حريز الذي يرويه الناس عن النبي صلى الله عليه وآله وسلم أنه قال لعلي أنت مني بمزلة هارون من موسي حق. ولكن أخطئ السامع قلت فما هو ؟ فقال إنما هو بمنزلة قار‘ن من موسي "

Huraizu Yace Hadisin Da Mutane Suke Ruwaitowa daga Annabi saw Akan Ali,
Cewa Kana Matsayin Haruna Ga Musa Wurina Gaskiyane.
Sai Dai Mai Saurara Ne Yayi Kuskure.
Sai Nicce Masa Toh Ya Hadisin yake ?

Sai Yace " Kana Matsayin Qaroon Ne Gun Musa.

وكان يلعن عليا سبعين مرة بالغداة والعشي

Ya Kasance Yana LA'antar Imamu Ali Sau Saba'in Da Safe Saba'in Da Yamma.

Amma Duk Da Haka Sun Kace :- Amintattce Ce Hadissan sa Sun Cika Littafan Hadisi.

ISHAQA DAN SUWAIDU

ibnu Hajar Yace " Tahzibub Tahzib " 3/236

وكان يحمل على علي تحاملا شديدا. وقال : لا أحب عليا "

Ya Kasance Yana Zagin Ali, Zagi Mai Tsanani. Yana Cewa :- Banson Ali.

amma Yahaya Dan Ma'in Yace " Amitatce ne "

KHALEED DAN SALMATU ALFA'AFA'IY

Ibnu Hajar Yace " Tahzibub Tahzib " 2/92

وكان يقول أبقض الخلافاء الي أبو الحسن

Ya Kasance Yana Cewa :- Mafi Qiyayyar Halifofi Gareni Baban Hassan.

ma'ana Yafi Qin Imamu Ali Akan Kowa, Amma Sukace " Amintattce Ne "

Ibnu Hajar Yace Cikin Muqaddimatul Fathu 1/ 428

وكان يبغض عليا
Ya Kasance Yana Qin Ali.

Kai Wannan Zindiqin Har Annabi Muhammad Saw Yake Zagi Amma Sun Wassaqashi Saboda Yaron Bani Umayya Ne.

Ibnu Hajar Yace

وذكر ابن عائشة أنه كان ينشد بني مروان الأشعار التي هجي بها المصطفى صلى الله عليه وآله "

Dan A'isha Ya Fadi Cewa Wannan Zindiqin Ya Kasance Yana Rairema Bani Marwan Waqoqin Da Aka Zagi Annabi Saw Cikinsu.

Innalillahi Wa'inna Ilaihi Raji'una !
Zindiqi Mai Zagin Annabi Saw Ana Kiransa Amintattce Ana Karbar Hadissansa !!

Dole Al'umma Su Shiga Cikin Matsala Matuqar Akwai Hadissan Wannan Zindiqi Cikin Littafan Msulunchi.

ABDULALLAHI DAN SAALIMU ALSH'ARIY

Ibnu Hajar Tahzibub Tahzib " 4/228

وكان يقول :- إن عليا أعان على قتل أبب بكر وعمر

Ya Kasance Yana Cewa :- Haqiqa Ali Ne Ya Taimaka Wurin Kashe Abubakar Da Umar.

Shima Wannan Sukace " Amintattce Ce "

Yakai Mai Karatu Adali Ya Kamata Ka Tambayi Kanka, Wai Miyasa Ire iren wadannan Mutane Ake Wassaqasu ?

Mi yasa Ake Girmama su ?

Shin Wane Kallo Kakewa Mai Zagin Sahabbai, Sannan Wani Irin Kallo Kakewa Wanda Ya Kashe Ahlin Gidan Annabinka ?

Ya Kake Kallon Mai Yimusu Wannan Zagin ?

Su Waye Suka Koya Musu Wannan Zagin ?

Waya Daure Musu Gindi ?

Ya Wajaba Kawa Kanka Wadannan Tambayoyi, Sanin Amsarsu Zai Taimakeka Wurin Sauqaqama Rayuwarka Adawar Banbancin Mazhaba, Aqeeda Da Fahimta !!

 KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post