@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
HATTARA DAI MALAMAN AHLUS-SUNNATI
Wani sahabi ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.W )menene gaskiya ? Sai ya amsa masa da cewa ya tambayi zuciyarsa , duk abinda ya ji ya kwanta masa a cikin zuciyarsa. Qarya kuma ita ce abinda yake jin kokontonsa cikin zuciyarsa ko da kuwa anyi masa fatawa an yi masa fatawa (ba zai ji ya gamsu da wannan abin ba ).
Yanzu anzo gurin, domin iyaye mata da 'ya'ya mata (daughters)sun soma kokawa game da yadda ake shigar da 'yan'uwan mamaci suna yin tarayya dasu cikin kaso (share ).
Yadda matsalar ke faruwa shine , idan mamaci ya rasu bai bar da namiji (son )ko Uba (father )ba, to, anan sai a shigar da 'yan'uwan mamaci su ci gado tare da uwar mamaci ko 'ya'ya mata (daughters )na mamaci , kuma yin hakan zalunci ne da danne haqqi , domin 'yan'uwa ba su da kaso cikin gadon dan'uwansu matuqar yana da uwa ko 'ya (daughter )a bayansa.
Hadisai kam ana iya canza su da bin son zuciya , amma Qur'ani Allah yayi alqawarin kare kayansa ta yadda qarya ba ta zuwa ta gaba gare shi ko baya gare shi . Saboda haka wannan hukunci na nan cikin Qur'ani .
Shi hukuncin 'yan'uwa da kakanni wajen gado tamkar hukuncin gadon 'ya'ya da ubanni ne, shi yasa matuqar akwai wani cikin iyaye ko 'ya'ya, to, 'yan'uwa ba za su taba samun wani kaso ba har abada.
Wannan hukunci nanan cikin aya ta 11 da 176 cikin suratul Nisa'i .
KU SHIRYA AMSAR DA ZA KU BAWA ALLAH RANAR GAMONKU DA SHI .
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~19th May, 2020.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Ahkamul islam
