@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KADA KU YAUDARI KANKU DA SAURAN JAMA'AH MANA
Ba zai zama laifi ba na tunatar da ku kamar yadda kuka ce tunatar da al'umma kuke yi cikin tafiyarku don neman uzuri .
Na kanga kuna daga jijiyar wuya musamman in 17 ga watan Zul-Hijja (YAUMUL GHADEER )ya zagayo da sunan cewa kuna nunawa jama'a haqiqanin wanda Annabi (S.A.W.W )ya nasabta a matsayin wanda zai ga je shi a bayansa , kuma kuna cewa babu wani guri wanda Annabi zai tafi face ya bar wani a matsayin magaji.
Cikin wannan hujjoji naku kuke kawo kwanciyar da Sayyidina Aliyu (R.A )yayi kan gadon Annabi (S )yayin hijra da kuma yayin yaqin Tabuka .
YAUDARAR DA KUKE YIWA KANKU
Yau shekara 5 kenan da fadawarku cikin rudani na rashin jagora cikinku sakamakon fadawarsa hannun azzalumai kamar yadda kuke cewa.
Sannan naga Annabi Musa (A.S )na raye ya sanya Annabi Haruna (A.S )ya kasance mai kula da tafiyar da al'ummarsa kafin ya dawo cikinsu, kuma ku ma kuna fadin haka a bakunanku .
Amma sai naga yanzu idanuwanku sun rufe, qwaqwalenku sun gauraya da jini, hankalinku ya bace, tunaninku ya gurbace ta yadda kuka kasa fahintar cewa ashe idan babu jagora ko shugaba cikin tafiya dole a sami wakilin wannan jagora wanda sai jagorance kafin ya dawo .
Sai naji kuna cewa yanzu ba ku da jagora wanda za ku riqa ji ko karba daga gare shi sai Zakzaky , alhali kuwa ba ya cikinku da gangar jiki .
Kuma kunyi qarya kuce cikin kashi 90% naku kuna iya ganawa da wannan jagora naku.
TAMBAYA
Shin, yanzu daga ina kuke karbar umarni cikin dukkan abinda kuke gudanarwa da sunar Harka ?
Anya ba shaidan ne ke jagorantarku cikin ayyukanku ba a halin yanzu ?
KADA KU YAUDARI KANKU 'YAN SHI'AH
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~17th May, 2020.
Tags:
Tunatarwa
