Ta Hanyar Miyagun Shawarwari Ake Dirar Wa Bayin Allah!!!




@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

HAQURI DA ADDU'AH CE MAFITAR MUMINAI

Alqawarin Allah ne cewa zai daukaka bayinsa muminai ta hanyar qasqantar da fajirai azzalumai , wannan dalili yasa azzalumai ke qoqarin ganin bayan muminai don neman dawwama kan karagar mulkinsu na zalunci , sai dai a qarshe su ke daukar qasqanci da tozarta .

Fir'auna (L.A )yayi yunqurin kawo qarshen Musa (A.S )da mabiyansa ta hanyar yin amfani da qarfin mulki , kuma Musa (A.S )ya gargadi mabiyansa da cewa su nemi sabati tare da yin haquri a matakin nasara .

Allah (T )na cewa:

👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻

‘’ Kuma mashawarta daga mutanen Fir'auna suka ce: ‘’ Shin, za ka bar Musa da mutanensa don suyi barna a cikin a
qasa (na tabbatar da addinin Allah ), kuma ya barka da Gumakanka (constitution )?‘’ Yace; ‘’ ZA MU YANYANKA 'YA'YAYENSU MAZA , KUMA MU RAYA MATANSU, KUMA LALLE NE MU MA SU RINJAYE A KANSU.

Musa ya cewa mutanensa ; ‘’ KU NEMI TAIMAKON ALLAH (ta hanyar yin addu'ar neman sabati ), KUMA KU YI HAQURI (kan wannan jarrabawa ). LALLE NE QASA TA ALLAH CE YANA GADAR DA ITA GA WANDA YAKE SO DAGA BAYINSA , KUMA KYAKKYAWAN QARSHE GA MASU TAQAWA YAKE.‘’

Suka ce; ‘’ An cutar damu gabanin ka zo mana, kuma daga bayan ka zo mana.‘’ Yace; ‘’ AKWAI TSAMMANIN UBANGIJINKU YA HALAKAR DA MAQIYANKU, KUMA YA SANYA KU KU MAYE A CIKIN QASA (a matsayin jagorori ), SANNAN YA DUBA (ya ga )YADDA KUKE AIKATA (irin naku aikin ).‘’

(A'ARAF: 27-29)

IDAN KACE WANE BAI IYA BA, KAI ALLAH NE YACE KA IYA?

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda .

        09039791509

~18th May, 2020. KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com

KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post