@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @
KA TSAYA A MADADINA CIKIN JAMA'ATA IN JI MUSA (A.S )
Allahu akbar, bisa sanin irin hali na jama'a (mabiya )da kuma hukuncin Allah yasa dukkan wani Annabi da zai bar cikin jama'arsa na wani lokaci gajere ne ko mai tsaho, to, ba zai bar wannan jama'a tasa kara-zube ba, dole sai ya aiyana wani wakili nasa amintacce wanda zai riqe masa amana har zuwa dawowarsa .
Ba lalle ne kowa yabi wannan wakili ba, amma haqqi ne a bar shi cikinsu don yankan hanzari da kuma jagorantar shiryayyun cikinsu .
Allah (T )ya bamu wannan labari cikin littafinsa mai tsarki game da Annabi Musa (A.S ), inda yake cewa:
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
‘’ Kuma mu kayi wa'adi ga Musa da dare talatin , kuma muka cika su da goma, sai miqatin Ubangijinsa ya cika dare arba'in. Kuma Musa ya cewa dan'uwansa Haruna: ‘’ KA MAYE MIN A CIKIN MUTANENA , KUMA KAYI GYARA (cikinsu ), KUMA KADA KA BI HANYAR MASU FASADI (wadanda ba son gyara ne a gabansu ba ).‘’
Haka abin ya kasance , Haruna ya tsaya kyam kan wannan umarni na jagoransa , amma hakan bai hana wasu suka juya baya ba, shi kuma bai fasa gyara ba har Musa (A.S )ya dawo cikinsu .
Imam Ali (A.S )ma ya bi irin wannan tafarkin ne, domin a yayin da jama'ah suka bijire masa bai fitinu ba, sai ya cigaba da gyara har lokacin da ya koma ga mahaliccinsa . To, kamar haka ne ke faruwa ga dukkan wani mujaddadi.
WANNAN CE HALAYYAR WAKILIN GASKIYA
Daga wakilanmu na Bauchi zone .
Tare da Ado Isah Guda.
09039791509
~18th May, 2020.
KU KARANTA WASU LABARAI ANAN>>>>>https://www.maasumah.com.ng/
IDAN KUNA DA WATA SHAWARA KO MAGANA DAMU KO AIKO MANA DA LABARI KU TURO MANA A ADRESHIN EMAIL: maasumalabari@gmail.com
KUBIYOMU A FACEBOOK DOMIN SAMUN LABARAI KUYI LIKE GASHI NAN AQASA
KU SAUKE MANHAJARMU TA WAYAR ANDROID DOMIN SAMUN LABARAI DA DUMI DUMI AWAYOYINKU KYAUTA KU LATSA LINK DIN DAKE QASA DOMIN YIN DOWNLOADING YANZU :/ MAASUMAH NIGERIA NEWS UPDATES ANDROID APPLICATION CLICK HERE FOR DOWNLOAD NOW
KUKARANTA WASU LABARAI ANAN
Tags:
Muhimman zantuka
