Shin, Wai Da Gaske Ne Mahaifan Annabi (S.A.W.W) Na Wuta???





@ MA'ASUMAH NIGERIAN NEWS UPDATED @

YANA DAGA CIKIN HADISAN QARYA DA AKA QIRQIRO DON CIN ZARAFIN MANZON ALLAH (S )

Akwai buqatar yin nazari cikin hadisan da ahlus-sunnah ke kawowa cikin littafan su, domin qiyayyar su ga Annabi (S.A.W.W )da iyalan gidansa (A.S )ta yi tsanani cikin zukatansu ta yadda ba za su iya boye shi ba.

Kaf cikin sahabban Annabi (S )babu wanda aka ruwaito wani hadisi dake nuna cewa mahaifansa 'yan wuta ne ,sai dai wani wanda ba a ambaci sunansa ba. Yadda abin ya faru shine, wai akace wata rana ya tambayi Manzon Allah (S.A.W.W )cewa a ina mahaifinsa yake? Sai Annabi (S.A.W.W )yace:

‘’ BABANA DA BAKANKA SUNA WUTA .‘’

Kunga anan ko ba komai an boye sunan wannan sahabi don kada a riqa ganin mahaifinsa dan wuta.

Amma mahaifan Annabi (S )da nahaifin Imam Ali (A.S )qarara aka kama sunansu cewa 'yan wuta ne. Ga hadisin kamar haka;

Imam Ahmad Bn Hambal ya ruwaito da kyakkyawan isnadi zuwa kan Ibn Buraidata , daga babansa yace;‘’ Mun kasance tare da Annabi (S )a wata tafiya , sai muka sauka, mu mahaya (riders )munyi kusan mutane 1000, mu kayi sallah raka'a biyu, sannan ya juyo gare mu idanuwansa na cike da hawaye.

Sai Umar Bn Khaddab ya miqe zuwa gare shi, sannan yace;‘’ Yaa Ma'aikin Allah , menene gare ka ?‘’ Yace;

‘’ Lalle na roqi Ubangijina ne cikin nemawa mahaifiyata gafara, amma bai bani izni ba, shene idanuwana ke kuka saboda tausaya mata daga wuta. Lalle ni na hane ku da abubuwa 3, na hane ku da yin ziyarar qabari, yanzu ku ziyarce shi domin ziyarar taku za ta tuna muku alkhairi ......‘’

(Musnad Ahmad , J:5, SH:355).

         TAMBAYA

Yanzu ko da ace gaskiya ce wannan magana, me yasa ba a kawo sunayen iyayen wasu da suka mutu kafirai ba sai su?

Ko duk iyayen sahabbai sun mutu da imani ne?

Daga wakilanmu na Bauchi zone .

Tare da Ado Isah Guda.

          09039791509

~29th May, 2020/ 8-10-1441.

Post a Comment


Yi Comment domin ka bayyana ra'ayinka akan wannan labarin anan akasa

Previous Post Next Post