Abbagano ✍️
Su Sayyid suna cewa babban abinda yafi musu daɗi a duk duniya shine, (SALLAH)
Wanda abin haushi idan ka ɗauke mu matasa zakaga mu kuma abinda yafi bamu Haushi shine sallah, domin zamu iya share awanni muna zaune muna surutai, amman dazarar anyi kiran sallah sai kaga fuskokin mu sun canja.
Lokacin da su Sayyid suke magana, da matasa, sai suke ce musu, batun sallar dare, muna iya cewa matashi, ko makara yayi Lalle idan ya tashi to ya rama.
To wannan dangane da sallar dare kenan, to wanda mukuma farillar ma dakyar muke yi.
Acikin littafan mu, akwai magana akan sallah kashi kashi, wanda sai ankarɓi sallah ne ma sannan za'a duba sauran aiyukan mutum.
Amman a hakan zakaga wasu daga matasan mu, basu damu suyi Sallah ba, ko kuma basu damu suyi ta da wuri ba.
Arhali yazo a hadisi, cewa:- mafificiyar sallah shine yinta akan lokacin ta.
Akwai ƙissar wani mutum, daya hango ɗansa daga saman bene zai faɗo, gashi shi kuma yana nesa da benan, amman sai ya miƙa hannun sa yace ya Allah, kawai sai ga yaran ya faɗo a hannun sa.
Lokacin da aka tambaye shi, sai yake cewa, shi tunda yake Allah bai taɓa kiran sa, yaƙi amsawa ba, saboda haka ne shima yasan mutuƙar yakira Allah zai amsa masa.
Sannan akwai wasicin da Imam Mahadi yayi wa wani ɗalibi da motar su ta lalace a tsakiyar jeji, gashi kuma sun kusa shiga jarrrabawa.
Sai Imam yace yaje su duba motar su zasu ga mai, su tuƙa su tafi, sai yace masa kai wanene? Sai yace nine Mahadi.Sai mutumin yace damai zakai mun wasiya? Sai Imam yace masa da Sallah akan lokacin ta.
Su Sayyid sukace sunyi shekara sama da 40 suna bautar Allah da yaƙini!!!
GAREMU MATASA
Tags:
Jagoran Gaskiya